✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ma’aikatan asibiti ke wulakanta majinyata

Wata mai jego ta ce ma'aikatan jinya sun yi ta marinta a lokacin da take nakuda.

Majinyata da dama da ’yan uwansu na yawan kokawa kan irin karbar da ake yi musu a asibitoci mussamman na gwamnati, inda idan mutum bai daure ba, zuciya za ta iya dibarsa ya doki ma’aikaciyar jinya ko ya hauta da masifa.

Sai dai kasancewar ma’aikatar lafiya na da muhimmanci a rayuwar mutane da kuma gudun kada su yi wa majinyata mugunta.

Hakan kan sanya mutane su hadiye bakin cikinsu su amince da wulakancin da ake yi musu.

Wata mace mai suna Hajara Abubakar ta shaida wa Aminiya cewa ta taba kai danta a sume zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya taTarayya da ke Yola.

Da ta je da shi a sume sai ta tarar da wata ma’aikaciyar lafiya sanye da kayan aiki tana waya, kuma duk ihun da take yi hakan bai sanya ma’aikaciyar ta ajiye wayar da ke hannunta ba sai da ta gama abin da take yi sannan ta duba su a wulakance kamar ba dan Adam aka kawo mata ba.

Dakin haihuwa

Ita kuwa A’isha Haladu cewa ta yi akwai lokacin da nakuda ta dauke ta sai aka kai ta Asbitin Kwararru da ke Jihar Adamawa, suna shiga dakin haihuwa sai nakudar ta karu, sai ihu take.

Jin haka sai wata ma’aikaciyar lafiya ta ce da ita, “Ki rufe mini baki, a lokacin da kike jin dadi ai ba ki yi ihun nan ba.”

A cewar Hafsatu Abdullahi kuma ita da ta zo haihuwa a Asibitin Kwararrun, ban da marin ta babu abin da ma’aikatan lafiyar suke yi.

Ta ce ga azabar haihuwa sannan ga ta mari.

A cewarta, kamata ya yi a kowace ma’aikatar kiwon lafiya a samu masu daukar rahoton duk wata ma’aikaciya da take aikata irin wannan domin fuskantar doka.

Wani mai suna Malam Modibbo Kawu ya ce su makiyaya da zarar an gan su ko da ido a kalle su ba a yi, sai ma’aikatan sun gama abin da suke yi sannan su kalli mara lafiyar suna tambayoyi marasa amfani.

Misali sukan tambaya ko marar lafiyar na shan giya. “Ina ni ina shan giya balle matata mu da muke Musulmi ai wannan isgilanci ne,” inji shi.

Dalilin da na daina taimako –Likita

Da Aminiya ta tuntubi wani likita Dokta Muhammad Bashir ya ce a lokacin da ya fara koyon aikin likitanci an tura shi wani asibitin koyarwa, kuma saboda yadda yake tausaya wa marasa hali sai wata ya kare ya ga ba ya da ko sisi a asusunsa na albashi.

Hakan ya sanya yau da gobe ya sanya shi ba ya tanka wa wanda zai kawo majinyaci a gigice babu ko sisi.

Da aka tambaye shi game da wulakanta mutane da ake zargin ma’aikatan jinyar da yi, sai ya bushe da dariya ya ce babu wani ma’aikacin lafiya ko likita da zai wulakanta wani sai da dalili ko an umurce su da su kawo kudin aiki ko na magani ba su yi ba, sannan sai su shiga ihu da kukan a taimaka musu.

“Kin ga idan mutum bai kawo kayan aiki ba, ta yaya likita ko wata ma’aikaciyar lafiya za ta taimaka, domin duk taimakon da ka ba da kamar ba su magunguna kyauta, asibiti zai ci ka tarar da sai ka gwammaci rawa da kidi.”

‘Hauka muke manna musu’

Wata ma’aikaciyar lafiya Malama Hasiya Jibo ta ce wadansu majiyantan ko ’yan uwansu ne ke da da gautsin magana har suke fusata ma’aikatan jinyar su yi musu ba daidai ba.

“Mutum ne ya kwana yana aiki har gari ya waye babu barci ga kuma kasala sannan sai wata ko wani ya sake magana kamar saukar markade. Tunda ba za ka iya marinsu ba ai sai ka manna musu hauka,” inji ta.

Da Aminiya ta tambaye ta kan zargin wulakanta mata a dakunan haihuwa sai ta ce, “Wadansu matan ne ba su da fasali.

“Sai mu yi ta fada musu kada su hade kafafunsu amma sai su ki ji. Idan ba muna daka musu tsawa ba kin ga za su iya kashe dan da za su haifa wajen shake masa wuya”.

Ta kara da cewa, “Na taba marin wata mata saboda tana kokarin kashe danta. Daukar ciki da laulayinsa na wata tara ga wahalarsa sannan ranar karshe sai su so su kashe dan.”

‘Sakacin ma’aikatan jinya ya yi yawa’

Ita kuwa Hajiya Zainab Sulaiman ta bayyana wa Aminiya cewa saura kiris sakacin malaman asibiti ya janyo jikanta ya rasa kafarsa.

Ta ce bayan da jikanta ya samu karaya sai aka yi masa aiki a Asibitin Kwararru na Murtala da ke Kano inda ta zauna a asibitin don jinyar yaron.

Hajiya Zainab ta kara da cewa, “Ba zan taba manta lokacin da wannan abu ya faru ba, lokacin da aka zo kwance dinki sai likita ya ce aiki fa ya lalace domin an samu matsala wajen wankin ciwon.

“Yaron nan ya sha wuya sosai domin sai da aka sake yi masa aiki sannan kafar ta warke,” inji ta.

Hajiya Zainab ta dora alhakin faruwar hakan kan sakacin malaman asibiti wadanda ke kula da yaron.

“A gaskiya zaman da na yi na jinyar yaron a asibiti na ga yadda suke mu’amala da mutane.

“Yawanci koda wata matsala ta taso masu jinyar tsoro suke su tunkari malaman asibitin don gudun wulakancin da zai iya biyo baya.

“Idan mutum ya je ya yi musu magana a kan su zo su duba marasa lafiya musamman da daddare, to sun fara fada ke nan wai an hana su barci da sauransu,” inji ta.

Sai da na bude wuta a asibitin’

Wata mai suna Malama Hauwa Tijjani ta ce ta fuskanci sakaci daga malaman asibiti a lokacin da ta taba zaman jinyar ’yarta a wani asibiti da ba ta bayyana sunansa ba saboda wasu dalilai.

Malama Hauwa ta ce sai da ta kai sun yi fada da malaman asibitin sannan suka samu sauki.

“Sai da ta kai na bude musu wuta sannan suka shiga taitayinsu suka dauki aikinsu kamar yadda ya kamata.

“Tun farkon zuwana dakin na lura da yadda ma’aikatan da ke dakin ke yin banza da aikinsu.

“Abin yana yi min ciwo. Wata rana sai jikin yarinyata ya rikice na tafi da sauri zan sanar da su, shi ke nan sai suka yi kaina suna yi min fada.

“Ai kuwa haushi ya kama ni, na fara fada ina cewa ai da bazarmu suke rawa, ba don mu ba, ba za su zo wurin ba ballantana a biya su albashi.

“Ke har barazana na yi musu cewa sai na sanar da hukumar asibitin abin da suke yi a dakin, daga nan dai suka shiga ba ni hakuri, sannan na kyale su,” inji ta.