✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da manyan kungiyoyin Turai ba sa son sayen Ronaldo

Bana Ronaldo da Man-U ba za su buga Gasar Zakarun Turai ba kuma babu wata babbar kungiya da take son daukar sa a nahiyar

Shahararren dan kwallon kafar duniya, Cristiano Ronaldo, ya shaida wa Manchester United a baya-bayan nan cewa yana son barin ta, sai dai kuma babu kungiyar da ta nuna sha’awar sayen sa.

Har yanzu dan wasan bai koma kungiyarsa domin fara atisaye ba don tunkarar sabuwar kakar wasanni ta bana, sakamakon wani uzuri da ya shafi iyalinsa.

Atletico Madrid

A baya-bayan nan an yi ta rade-radin Ronaldo na iya komawa kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, sai dai abun kamar da wuya duba da irin adawa mai zafi da ke tsakaninsa da kungiyar lokacin da yake murza wa Real Madrid leda wanda su ne manyan abokan hamayyarsu a birnin Madrid na kasar Andalus.

Juventus

Da wuya Juventus ta sake sha’awar daukar Ronaldo duba da cewar a baya ta saye shi daga Real Madrid da zummar ya jagorance ta wajen lashe Gasar Zakarun Turai (UEFA Champions League), amma kwalliya ta gaza biyan kudin sabulu.

Daga bisani Ronaldo ya bar Juventus ba tare da ba ta isasshen lokacin maye gurbinsa da wani dan wasan ba.

Paris Saint-Germain

Da kamar wuya PSG ta sayi Ronaldo a bana duba da irin tarin manyan ’yan wasan da take da su irin Mbappe, Neymar, Messi, Ramos da sauransu wadanda suke lakume kudade masu yawan gaske a kungiyar.

PSG ba za ta dauki Ronaldo ba duba da irin albashi mai tsoka da yake karba, wanda hakan zai zama babban kalubale wajen cinikayyarsa.

Barcelona

Barcelona ba ta da matsala wajen sayen tsofaffin ’yan wasa, musamman wanda suka tara shekaru.

A baya-bayan nan ta sayi Lewandowski daga Bayern Munich, amma cinikayyar Ronaldo kamar auren gurguwa a nesa ne.

Dalili kuwa shi ne Ronaldo na daga cikin manya-manyan abokan hamayyar Barcelona, musamman lokacin da yake Real Madrid.

A lokuta da dama a baya an sha tada jiyoyin wuya da shi idan kungiyoyin biyu suna barje gumi da juna.

Kazalika, Barcelona na fama da matsalar kudi, wanda hakan ne ya sa ta zaftare albashin ’yan wasanta da dama don samu rarar kudin gudanar da kungiyar.

Chelsea

Tun da fari, an yi tunanin Chelsea za ta sayi Ronaldo, duba da cewar kungiyar ta samu sabon shugaba kuma wanda yake da sha’awar tara manyan ’yan wasa a kungiyar.

Sai dai wannan alaka ta samu cikas, saboda kocin kungiyar Thomas Tuchel ya nuna ba ya sha’awar aiki da Ronaldo.

Hakan ya sa zancen ya bi iska.

Real Madrid

Tun bayan da Mbappe ya ki amincewa ya je Madrid aka fara hasashen Ronaldo na iya komawa gidansa na tsamiya.

Amma Real Madrid ta karyata rade-radin da aka yi, inda ta nuna a yanzu ta fi sha’awar sayen ’yan wasan da za su dauki lokaci ana damawa da su a harkar tamola.

Manchester City

Wakilin Ronaldo, Jorge Mendes, ya yi wa Manchester City tayin Ronaldo kuma shugabannin kungiyar sun nuna sha’awar sayen sa a bara, amma kocin kungiyar, Pep Guadiola, ya ki bude kofar daukar sa.

Hakan ne ya sanya Manchester City sayen dan wasan gaban Dortmund, Erling Haaland, lamarin da ya sanya maganar Ronaldo ta bi rariya.

Liverpool

Kungiyar ba za ta taba neman Ronaldo ba bisa dukkan alamu.

Dalili kuwa shi ne Liverpool ita ce babbar abokiyar hamayyar Manchester United a Ingila.

Wannan adawa tasu ta sanya ko hada neman cinikayyar dan wasa ba sa yi bare kuma kasuwanci ya wakana a tsakaninsu.

Tuni Liverpool ta ware makuden kudade ta sayi Darwin Nunez daga Benfica, bayan ta sayar sa fitaccen dan wasanta Sadio Mane ga Bayern Munich.

Bayern Munich

Bayan Munich ta sayar da Lewandowski ga Barcelona an shiga rade-radin ko za ta maye gurbinsa da Ronaldo.

Amma ina! Tuni ta yi wa wannan rade-radi burki, inda shugabanta Oliver Khan, ya ce “Ronaldo na daga cikin manyan ’yan wasan duniya da nake mutuntawa, amma ba zai dace da tsarinmu ba.”

Bisa dukkan alamu dai Ronaldo ba zai buga gasar zakarun turai ta bana ba, duba da cewa Manchester United ba za ta je gasar ba.

Ga shi kuma babu wata babbar kungiya daga nahiyar Turai da take son daukar sa a matsayin sabon dan wasanta.