✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalilin da Maroko ta sa Ronaldo kuka, ta kora Portugal gida

Tun a zagayen farkon wasan Portugal ta nemi yi wa Maroko shigar sauri, amma yunkurin Joao Felix ya kare a tutar babu

Gwarzon Dan Kwallon Duniya da ya lashe Gasar Ballon d’Or sau biyar kuma Kyaftin din Portugal, Cristiano Ronaldo, ya barke da kuka bayan tawagar ’yan wasan Atlas Lions na Maroko ta yi musu kwaf-daya, ta kora su gida a Gasar Kofin Duniya.

Maroko ta kafa tarihin zama kasar farko a nahiyar Afirka da ma yankin Larabawa da ta kai matakin Kusa Da Karshe a tarihin Gasar Kofin Duniya, bayan ta doke Portugal da ci daya mai ban haushi, ta hannun dan wasanta, Youssef En-Nesiry a minti na 42.

Da alama kuma da wannan kifa-daya-kwala da El-Nesiry ya yi wa Portugal a Filin Wasa na Al-Thumama a rana ta 19 ta Gasar Kofin Duniya Karo na 22 da ke gunada a kasar Qatar, Cristiano Ronaldo, ya ci taliyar karshe a wasannin Gasar Kofin Duniya.

Abin da ya sa Ronaldo kuka

Tsohon dan wasan gaban kungiyar Manchester United, Owen Hargreaves, ya ce abin da ya sa Ronaldo kuka bayan Maroko ta fitar da su, shi ne ganin cewa babban abokin hamayyyarsa, Lionel Messi na Argentina ya samu damar kaiwa matakin dab da karshe, da yiwuwar cin kofin.

Idan hakan ta faru, a yayin da Cristiano mai shekara 37 ya halarci gasar ta karshe, to magana ta kare a mahawar da ake yi na cewa tsakanin shi da Messi, wane ne dan wasan da ya fi kowa?

Owen ya ce, “Idan Messi ya ci Kofin Duniya bayan ya ci Cuppa America, to akwai magana [wane ne ya fi zama gwani?]

“Shi zai fi kowa, kuma dole Ronaldo ya ji zafi… ba sa shiri, ga shi sun yi kankankan a Gasar Zakarun Turai da Ballon d’Or, yanzu kuma abokin adawarsa ya yi gaba, yana buga kowane wasa kai kuma an cire ka, ai dole Ronaldo ya ji zafi.”

Yanzu haka dai, tawagar ’yan wasan Atlas Lions na Maroko za su fafata da Faransa mai neman kare kambunta, a wasan kusa da na karshe na Gasar Kofin Duniya da ke gudana a kasar Qatar.

Wasan Maroko da Faransa ya dauki hankali matuka, ganin cewa kowacce daga cikin kasashen biyu na neman kafa sabon tarihi.

Maroko na neman dorawa a kan sabon tarihin da ta kafa na zama ta farko a Afirka da Yankin Larabawa da ta kai matakin; Hasali ma, duk abin da ta yi, ta bar tarihi.

Yanzu dai yawancin masoya kwallon kafa a Afirka da yankin Larabawa sun tattaru a kan goyon bayan Maroko, wada za ta fafata da uwar rikonta na mulkin mallaka, Faransa.

Faransa kuma na neman kafa tarihin zama ta hudu a jerin kasashen da suka taba kare kofin gasar da aka fara tun daga shekarar 1930.

Yanzu shekara 60 ke nan rabon da a samu kasar da ta kare kofin tun shekarar  1962 da Brazil a kare kambunta.

Maroko ta ba da mamaki

Tawagar ’yan wasan Maroko ta kara ba da mamaki a wasansu na ranar Asabar, duk da cewa zaratan ’yan wasanta hudu ba su samu bugawa ba.

Bugu da kari, alkalin wasa ya sallami dan wasan Atlas Lion daya, Walid Cheddiira, a yayin da ake saura minti biyar a tashi daga karin lokacin da aka yi.

Alkali ya ba wa dan wasan Maroko jan kati minti biyar kafin tashi daga wasan karin lokaci. (Hoto: Fifa Plus).

Tun a zagayen farkon wasan Portugal ta nemi yi wa Maroko shigar sauri, amma yunkurin Joao Felix na zura mata kwallo a raga ya tashi a tutar babu, golanta, Yassine Bounou, ya yi caraf da ita.

Duk kokarin kocin Portugal, Fernando Santos, na amfani da Cristiano Ronaldo wajen kwatar kansu da kyar a hannun Larabawan, abin ya faskara, sai da Maroko ta dura musu taliyar karshe a ranar 10 ga watan Dismamba, 2022.

A minti na 42, daf da tafiya hutun rabin lokaci, Maroko ta girgiza ragar Portugal, ta hannun dan wasan gaban Sevilla, Youssef En-Nesiy wanda ya ci da ka, bayan Yahya Attiat-Allah ya yi masa kurosin.

A yayin da Larabawan na Afirka suka tsallaka zuwa Semi-Fainal, su ne suka dora kasashen Turai na Portugal, Belgium da Spain a jirgin komawa gida daga Gasar Kofin Kofin Duniya na farko da aka gudanar a yankin Larabawa.

Moroko ta kai Semi-Fainal

Yanzu dai a karon farko a tarihin Gasar Kofin Duniya ta FIFA, Maroko ta zama ta farko daga daga Nahiyar Afirka da Yankin Larabawa.

Za kuma ta fafata ne da Faransa, mai rike da kofin, lamarin da duniya ke son ganin yadda za ta kaya.

Yawancin jama’a na ganin ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare, duba da yadda kasar Larabawan ta yi ta bayar da mamaki a gasar ta bana, inda ta yi waje da manyan kasashen uku — Spain, Belgium, da Portugal.

Idan ba a manta ba, tun a farko-farkon gasar, Kasar Saudiyya ta ba da mamaki, inda a karon farko ta ci wasanta na farko gasar, ta hanyar doke Argentina.