✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalilin da matan fim ba su dadewa a gidan aure

Bayan shekara 14, Mansura da Sani Danja sun raba gari

A makon jiya ne aka wayi gari da labarin rabuwar aure a tsakanin fitaccen jarumi a Masana’antar Kannyood wato Sani Danja da fitacciyar jaruma, Mansura Isah.

Jaruman biyu sun kwashe kimanin shekara 14 a matsayin mata da miji, inda Allah Ya azurta su da ’ya’ya hudu.

Rahotanni sun ce jaruman biyu sun dade da rabuwa, amma sai a makon jiya ne Mansura ta saka a shafinta na Instagram, inda a nan din ma ta cire jim kadan bayan ta wallafa.

Amma sai dai duk da cirewar da ta yi, an riga an gani wanda hakan ya sa aka fara bibbiyar lamarin.

Duk kokarin Aminiya na gano dalilin mutuwar auren bai samu ba, domin duk wanda wakilinmu ya tuntuba, sai ya ce bai san dalilin ba.

Amma Aminiya ta gano cewa tuni Mansura ta kwashe kayanta daga gidan Sani Danja, inda ta koma gidanta.

Auren Danja da Mansura

A shekarar 2006 ce aka daura auren masoyan biyu a birnin Kano, sannan Allah Ya azurta su da ’ya’ya hudu, mace daya da maza uku.

Aure suka yi na soyayya, inda har ake kwatance da su ana yaba musu yadda suke nuna soyayya da kaunarsu a fili.

Sun taba yin kaura zuwa Abuja, sannan shi Sani Danja ya rika gudanar da harkokin wakoki da ’yan Kudu, kuma ya fada siyasa, inda aka rika ganinsa yana taya tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan kamfe a gaba-gaba.

Daga baya Mansura ta bude Gidauniya mai suna ‘Today’s Life Foundation’, inda a sanadiyar harkokin taimakon mabukata da take yi, ta samu kusanci da manyan mutane, ciki har da matar Gwamnan Jihar Kebbi Dokta Zainab Shinkafi Bagudu.

Hakan ya sa a lokacin zabe wadansu suka rika yabon ma’auratan biyu, inda mijin yake tallafa wa PDP, ita kuma matar take tallata APC.

An dade ana jifar matan Kannywood da cewa ba su cika zaman aure ba, inda da an samu jaruma ta yi aure, sai a fara cewa Allah Ya sa ta zauna.

A yanzu haka a masana’antar akwai jarumai mata da yawa da zawarawa, akwai kuma wadanda suka yi auren suka fito suka dawo masa’antar, da kuma wadanda bayan sun fito, sai suka koma gefe suka daina yin fim din baki daya.

‘Abin da ke kawo rabuwar aure’

Aminiya ta tuntubi wani masanin harkokin masana’antar ta Kannyood, wanda ya ce lamarin ya ta’allaka ne da yanayin lokaci, wanda a cewarsa ba wai a Masana’antar Kannywood ba ce kawai lamarin ya tsaya ba.

A cewarsa, “Da farko dalilin da yake hana matan fim zaman aure ba wani bakon dalili ba ne, dalili ne da yake shafar kowace irin zamantakewa a tsakanin al’umma.

Kuma ba za a ce matan fim duk ba sa zaman aure ba, domin ka ga auren Sani Danja da Mansura yau shekara 14 ke nan, shi ya sa rabuwar ma ba ta yi wa mutane da yawa dadi ba.”

Masanin wanda bai son a ambaci sunansa ya kara da cewa, “Rabuwar aure ta ’yan fim da  sauran mutane tana da alaka ne da sauyin rayuwa da mutane suke samu, ta yadda za ka ga kafin aure, akwai abubuwa da miji ko matar suka saba da su, yayin da zaman auren ka iya kawo cikas.

Akasari, laifin maza ya fi yawa, saboda ba sa iya bambance rayuwar aure da ta samartaka.

“Misali, babu macen da za ta jure ganin matan waje suna bayyana wa mijinta soyayya, tare da aiko masa sakonni da hotuna. A wasu lokuta sai ka ga namiji yana fadawa tarkon matan, duk kuwa da cewa ya san ba aurensu zai yi ba.

“A irin wannan yanayi ana samun rashin jituwa, shi namijin yana iya gaza tsare kansa, yayin da ita macen kuma take kasa fahimtar cewa yanayin sana’arsa ne ya sa dole mata su bibiye shi.”

Jaruman Kannywood da suka yi aure kuma har yanzu suke tare

Ba Mansura Isah da Sani Danja ba ne kawai jaruman da suka yi aure a Masana’antar  Kannywood. Akwai wadanda suka yi aure da dadewa kuma har yanzu suna tare, duk da cewa wadansu sun rabu.

Akwai Darakta Hassan Giggs da matarsa Muhibbat Abdulsalam, wadanda sun dade da aure kuma suna tare har yanzu da ’ya’yansu.

Akwai kuma Al’amin Ciroma da matarsa Wasila Ibrahim, wadda ta fito a fim din Wasila, kuma har yanzu tana zaune a gidan mijinta.

Ya ce, “Idan ka duba yanzu ai akwai aure-aure da aka yi a Kannywood kuma suna zaune da matansu, sun haifi ’ya’ya da yawa. Misali Al-Amin Ciroma da Wasila Ibrahim da Hassan Giggs da Muhibbat Abdulsalam da sauransu.”

‘Abin da ya  sa rabuwar Sani da Mansura ya ba mutane mamaki’

Ya kara da cewa, “Batun rabuwar Sani Danja da Mansura Isah abu ne da ya zo wa mutane  a matsayin ba-zata, domin suna cikin wadanda ake kafa hujja da su a cikin ’yan fim a matsayin ma’aurantan da suka dade ba su rabu ba, kuma Allah Ya yi musu arzikin yara hudu, mace daya maza uku.

“Sannan a daidai lokacin da sakin ya faru suna kusa da cika shekara 14 da aurensu, domin an daura aurensu ne a watan Yunin shekarar 2006, wanda ni kaina na samu halarta.”

Bayan Karamar Sallah suka rabu

Mai sharhin ya kara da cewa har yanzu ba shi da masaniya a kan dalilin rabuwarsu, “Babu wanda zai ce maka ga dalilin rabuwar, amma dai ya faru ne bayan Karamar Sallar nan da ta gabata, kuma tuni Mansura Isah ta bar gidansa da zama.”

‘Ba wannan ne karo na farko da Sani ya taba sakin Mansura ba’

Game da jita-jitar da ake yadawa cewa dama a baya sun taba rabuwa, mai sharhin ya tabbatar da haka, inda ya ce, “Wannan ba shi ne karo na farko da suka fara rabuwa ba, domin kusan shekara bakwai da suka wuce a baya Sani Danja ya taba sakin Mansura Isah inda suka dauki lokaci ba sa tare da juna sai daga baya aka shirya.”