✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalilin da matasan Najeriya za su mutu ba tare da samun aikin yi ba — Buhari

Matasa su tabbatar Najeriya ta zauna lafiya domin mutane su zo su zuba jari.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya sanar cewa akwai tarin matasa a kasar nan wadanda suka kammala karatun digiri a fannonin ilimi daban-daban kuma suka samu sakamako mai kyau, amma a karshe ba za su taba samun aikin yi ba.

Buhari ya yi furucin hakan yayin wata hira ta musamman da ya yi da Gidan Talabijin na ARISE da safiyar ranar Alhamis.

Shugaban ya gargadi matasan kasar da su gyara halayyarsu madamar suna son samun aikin yi, lamarin da ya ce muddin babu tsaro a kasar, matasa da dama za su mutu ba tare sun cimma muradunsu ba.

Ya buga babban misali da irin rawar da matasa ke takawa wajen haifar da rikici a kasar da zangar-zangar #EndSARS da aka yi a karshen shekarar 2020 da ta gabata, wacce ta razanar da masu zuba jari a kasar yayin da samun aikin gwamnati ke da matukar wahala.

A kan haka ne Shugaban ya ce, irin wannan mummunar dabi’a da matasan kasar ke yi ce za ta haifar da “mutum ya samu kyakkyawar shaidar digiri amma har ya mutu ba zai samu aikin yi ba.”

A cewarsa, “Ka je wurin kowane Gwamna a yanzu kana neman ya baka kwangila ko aikin yi, zai ce maka babu, kuma hakan take har ga Kananan Hukumomi.

“Saboda haka, za ka iya samun shaidar digiri mai kyau amma sai ka mutu ba tare da samun aikin yi ba kuma babu abin da ya janyo haka face fargabar da masu zuba jari a kasar ke yi na cewa babu zaman lafiya.

“Saboda haka, ina fada wa matasa cewa, idan har suna son aikin yi, su sauya dabi’unsu, su tabbatar Najeriya ta zauna lafiya domin mutane su zo su zuba jari.

“Dubi yadda ire-iren wadannan matasa suka kona sabbin motocin bas 200 wanda tsohon Gwamnan Legas ya sayo, saboda haka waye zai je ya zuba kudinsa a wurin da babu zaman lafiya? Ba mai yin haka.

“Abu ne mai sauki, ku sauya halayyarku ku kama kanku, sannan ku zauna lafiya, haka ne kadai zai sa mutane suka kawo kudinsu kasar,” a cewar Buhari.