✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Dalilin da muke so Gwamnan Bauchi ya yi takarar Shugaban Kasa’

Kungiyar ta ce ’yan Najeriya ba sa more romom dimokuradiyya saboda gazawar gwamnati

Wata kungiyar siyasa mai fafitukar samar da shugabanci na-gari (BAM-V) da ke goyon bayan tsayawar Gwmnan Bauchi, Bala Muhammed takarar shugabancin kasa a 2023, ta ce ’yan Najeriya ba sa more romom dimokuradiyya musamman gazawar gwamnati wajen sauke nauyin da ke kanta na samar da tsaro da walwalar jama’a.

Sanarwar da kungiyar reshen Jihar Kano ta fitar karkashin shugabanta, Adnan Mukhtar Adam ta ce Bala Muhammad shi ne dan takarar da ke da dukkanin abubuwan da shugaba ke bukata domin jagorantar Najeriya a 2023.

Ya ce Allah Ya huwace wa Najeriya arzikin jama’a da na albarkatu masu dimbin yawa, amma a cewarsa, son kai irin na shugabanni ya sa an kasa samun cigaban a zo a gani.

Kungiyar ta bukaci sauran ’yan takarar da ake so su fito a Jam’iyyar PDP don shugabancin kasa a 2023 kamar Alhaji Atiku Abubakar da Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso da Hassan Dankwambo da Sule lamido da su mara wa Bala Muhammed baya domin amfanin kasa baki daya.