✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalilin da muke son kwato Kano daga APC da PDP — Dokta Isyaku Rabi’u

Ai yanzu su tsofaffi sai dai mu dauke su a matsayin masu bayar da shawara.

Dokta Yusuf Is’hak Rabi’u malamin addinin Musulunci ne wanda yake da kwarewa a kan abin da ya shafi Bankin Musulunci.

Doktan kuma dan marigayi Khalifa Isyaku Rabi’u, da yake shirin fitowa takarar Gwamnan Jihar Kano a karkashin Jam’iyyar Action Alliance (A.A).

A tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana shirye-shiryen da yake da su ga jihar don kwace ta daga manyan jam’iyyun APC da PDP.

Jam’iyyarku tana cikin jam’iyyun da ba a san da zamansu a Jihar Kano ba idan aka kwatanta da PDP da APC. Yaya kake ganin za ku gamsar da Kanawa su zabe ta?

Gaskiya ne jam’iyyarmu ba a san ta sosai a Jihar Kano ba, amma tana daga cikin manyan jam’iyyu a kasar nan domin muna da ’yan Majalisar Wakilai.

Na yi imani cewa idan aka ci gaba da wayar wa jama’a kai mutane za su san jam’iyyar.

Baya ga niyyar alheri da jam’iyyar take da shi akwai tsare-tsarenmu da shirinmu a kan jihar, abu ne da zai janyo mana jama’a.

Za mu fara shirya taruurukan wayar da kai inda za mu gayyaci masu ilimi daga jami’o’i da dalibai da limamai da masu Keke NAPEP da sauran jama’ar gari domin mu sanar da su shirye-shiryenmu su samu damar yanke hukunci a lokacin zabe.

Idan ka zama Gwamanan Kano mene ne babban burinka, wadanne abubuwa za ka fi mayar a hankali a kai da zai su amfani jama’a?

Za mu mayar da hankali ne wajen yakar rashin aikin yi saboda yawancin matsalolin da muke fuskanta a wannan lokaci rashin aikin yi ne ya janyo su.

Kada a manta cewa Kano tana daga cikin manyan birane a kasar nan ta banagren yawan al’umma.

Muna magana ce a kan mutane kusan miliyan 20 haka kuma kashi 80 na wannan adadi matasa ne.

A shekarunka 42 ka shirya wa tunkarar matsalolin jiha kamar Kano?

Kwarai kuwa wannan shi ne ma dalili. Abin da muke kokarin yi shi ne a ba matasa dama, don haka gwamnatinmu za ta zama ta matasa.

Idan za mu iya tunawa a kwanakin baya an mika wani kudiri gaban majalisa wanda zai ba matasa damar tsayawa takara wannan kuma abu ne mai alfanu ga Najeriya domin idan mun duba tsofaffin shugabanni da suka yi aiki a kasar nan, za mu ga cewa sun yi ne a lokacin kuruciyarsu kamar su Yakubu Gowon da Janar Murtala Mohammed da Shehu Shagari da sauransu duk suna matasa lokacin da suka shugabanci kasar nan.

Tsofaffi sun fi mayar da hanakli wajen kula da kansu saboda harkar lafiya da sauransu.

Muna so mu zuba sababbin jini a harkar, kwamishinoninmu da shugabannin ma’aikatunmu za su kasance matasa.

Su kuwa tsofaffi sai dai mu dauke su a matsayin masu bayar da shawara.

Ka yi batun rashin gamsuwar mutanen Kano dangane da jam’iyyun APC da PDP, me ya sa kake tunanin mutane ba su gamsu da jam’iyyun ba?

Wannan ba wai ya shafi mutanen Jihar Kano kadai ba ne, idan aka duba gaba dayan kasar nan, mutane ba sa farin ciki da abin da yake faruwa.

Suna da sane da salon wannan gwamnatin musamman ma lamarin rashin tsaro da kuma tashin gwauron zabo na farashin kayayyakin abinci da man fetur da sauran abubuwa da mutane suke bukata.

Don haka idan muka samu shugabanci za mu gudanar da gwamnatin hadin gwiwa inda za mu tafi tare da ’yan kasuwa mu hada gwiwa da kwararru don ba mu shawawari kan yadda za mu tafiyar da al’amura don cim ma nasara.

Jihar Kano ta yi kaurin suna wajen amfani da ’yan dabar siyasa, ta yaya za ka gudanar da naka salon?

Ba mu da wani shiri na yin amfani da ’yan daba a harkarmu. Muna so mu canza harkar gaba daya yadda za mu kawo mutane masu inganci masu niyyar ci gaba da za su kawo mafita ga alumma.

Za mu yi kokarin mayar da su makaranta. Sannan za mu sama musu ayyukan yi domin kamar yadda na bayyana a farko rashin aikin ne ummul-haba’isin kowace matsala da muke fama da ita a kasar nan ba a Kano kawai ba.

Idan ya kasance mutum ba shi da abin yi to dole ne ya nema wa kansa aikin yi ko mai kyau ko akasainsa.

Mutane suna tunanin cewa yawancin ’yan takarar da suke kananan jam’iyyu sukan janye takararsu tare da goya wa ’yan takarar manyan jam’iyyu baya saboda wasu dalilai na …

Idan ka dubi mutanenmu da kuma tsare-tsarenmu da shiryeshiryenmu ka san cewa ba za mu janye saboda dalilai na kudi ko duk wani abu da za ka fadi daga manyan jam’iyyu ba.

Idan ka duba ai rashin tabuka abin kirki na wadancan manyan jam’iyyu ya sa muka zo don mu kawo agaji ga al’umma wajen yi musu abin da ya dace.

Don haka hankali ba zai dauka ba a ce mun fito don kawo canji sanann mu buge da bin wadancan jam’iyyu da suke da matsaloli.