✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Dalilin da muke zawarcin Tambuwal ya fito takara a 2023’

Tambuwal ya shiga cikin jerin fitattun mutanen da suka samu lambar yabo.

Shugaban Kungiyar Tambuwal Save Nigeria (TSN), Alhaji MD Yusuf ya ce suna zawarcin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sakkwato ya fito takarar Shugaban Kasa a shekarar 2023 ne saboda kyakkywan jagorancin da ya nuna tun shigarsa siyasa.

Alhaji MD Yusuf ya bayyana haka ne a yayin tattaunawa da manema labarai a Kaduna, inda ya ce ayyukan ciyar da kasa gaba da Gwamna Aminu Tambuwal ya yi, sun samo asali ne tun daga shekarar 2003 lokacin da ya je Majalisar Wakilai kuma ya shugabanci kwamitocinta da dama aka samu nasarori, zuwa lokacin da ya zama Shugaban Majalisar daga shekarar 2011 zuwa 2015.

Ya ce bayan Aminu Tambuwal ya zama Gwamnan Jihar Sakkwato ya kawo juyin-juya-hali a fannin ilimi a jihar ta hanyar bai wa ilimi muhimmanci, inda fannin ya samu kusan rubu’in kasafin da jihar ke kasaftawa duk shekara.

Kuma ya kafa gidauniyar bunkasa ilimi a karkashin Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar don kara karfafa ilimi, inda ye ce gidauniyar ita ce irinta ta farko a tarihin jihar.

Ya ce wannan namijin kokari na Gwamna Tambuwal ya fara haifar da da mai ido, inda yaran da a baya ba sa zuwa makaranta suke tururuwa zuwa, kamar yadda Asusun Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya tabbatar.

“Sannan jihar tana cikin na farko da suka fara biyan iyayen da suka sa ’ya’yansu mata a makarantun firamare alawus, domin karfafa ilimin ’ya’ya mata,” inji shi.

Shugaban ya ce gwamnatin Tambuwal ta kuma kebe Naira biliyan 7.5 domin bayar da tallafin karatu ga dalibai, baya ga ayyukan giggina makarantu da dama.

Ya ce a bangaren kiwon lafiya gwamnatin Tambuwal na gina Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Sakkwato da ake sa ran kammala wa nan da wata 26 kuma an dauki daruruwan leburori ’yan asalin jihar don yin aikin kuma akasarin kayan aikin ginin an samo su ne daga jihar da jihohin Zamfara da Kebbi.

Alhaji MD Yusuf ya ce gwamnatin jihar tana gina asibitocin kwararru a shiyyoyin sanatoci uku na jihar da Kwalejin Koyon Aikin Ungozoma a Tambuwal da Cibiyar Lafiya a Farfaru.

Shugaban ya ce ba a iya lissafa ayyukan hanyoyi da Gwamna Tambuwal ya yi ko yake yi a jihar inda ya kawo misali da aikin Titin Mai Tuta da na Unguwar Rogo zuwa Gagi da babban Titin Koko da sauransu.

“A bangaren matsalar tsaro, Gwamna Tambuwal na kokari don dakile ta’asar ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane a jihar,” inji shi.

Ya ce kusan duk bangaren da aka duba Gwamnan ya taka rawar gani wanda hakan ya sa “Gwamna Aminu Tambuwal ya shiga cikin jerin fitattun mutanen da suka samu lambar yabo ta manyan gidajen talabijin na Najeriya kan ciyar da jama’arsu gaba, inda ya yi zarra a tsakanin gwamnonin kasar nan 36,” inji shi.