✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da na kori ma’aikata 200  —Shugaban Karamar Hukumar Gwagwalada

Akwai wasu da kwata kwata ma ba su yi karatun ba amma an basu aikin da bai dace ba.

Shugaban Karamar Hukumar Gwagwalada da ke Abuja, Alhaji Abubakar Jibrin Giri, ya bayyana dalilinsa na korar wasu ma’aikatan karamar hukumar kimanin 200.

A cewarsa, ya kuma dakarta da wasu ma’aikatan saboda dalilai na rashin karatu.

“Akwai wasu da kwata kwata ma ba su yi karatun ba amma an basu aikin da bai dace ba.

Da yake ganawa da sarakunan gargajiya a yankin na Gwagwalada, Giri, ya ce akwai yawancin ma’aikatan da ke amfani da shaidar kammala karatu ta boge.

“Akwai wasu da kwata kwata ma ba su yi karatun ba amman an ba su aiki da bai dace ba.

“Amma muna mai shaida muku cewa in har muka kammala bincike da tsare tsare, duk wanda ya ci tantancewar da aka yi masa insha Allah zai dawo bakin aikin da aka ba shi,” a cewar Giri.

Giri, ya ce dalilin wannan zaman da ya yi da sarakunan shi ne wayar masu da kai game da  abubuwan da ke faruwa a tsare-tsare wannan sabuwar gwamnati.

Ya ce, ya ankarar da sarakunan ire-iren kalubalen da yake fuskanta a gwamnatinsa kuma cikin Yardar Allah zai shawo kan komai.

Daga karshe, Giri ya shawarci sarakunan da su kasance masu juriya da hakuri ga talakawansu.