Daily Trust Aminiya - ‘Dalilin da na yi garkuwa da kanwata na nemi a biya ni Naira
Subscribe

Hadiza Babayo da saurayinta Bala Sha’aibu

‘Dalilin da na yi garkuwa da kanwata na nemi a biya ni Naira miliyan 6’

Wata budurwa ’yar shekara 18 kuma ’yar asalin Karamar Hukumar Lafiyar Lamurde a Jihar Adawama mai suna Hadiza Babayo, ta sace ’yar baffanta a makaranta ce da nufin  a biya kudin fansar Naira miliyan shida don su yi amfani da kudin ita da saurayinta Bala Sha’aibu.

Da take zantawa da wakilinmu lokacin da take hannun ’yan sanda, Hadiza ta ce ta sace kanwar tata A’isha ce saboda tana son baffanta Alhaji Muhammad Modibbo Sarkin Fulanin Pindiga ya biya kudi domin tana son kudi don hidimar yau da kullum.

Sai dubunta ya cika bayan ta sace kanwar ce, bayan da yayan yarinyar ya lura cewa ita ce ta dauke ta, lokacin da ta bude nikabin da ta sanya don yarinyar ta gane ta.

“Ba aikina ba ne, tsautsayi ne ya kai ni ga aikata wannan laifi kuma a kan kanwata. Na yi da-na-sanin aikata wannan kuskure a rayuwa,” inji Hadiza.

Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa ba kamar yadda ta fada ba, Hadiza ta taba yin garkuwa da kanta a dakin saurayinta, inda ta buga wa iyayenta waya cewa an yin garkuwa da ita sai an biya kudi; kuma haka suka kukuta suka biya Naira miliyan daya da rabi sannan ta dawo gida.

Har ila yau wata majiyar ta ce ba wannan A’isha, ita ce ta biyar a yaran da ake zargin Hadiza ta sace, sai yanzu Allah Ya tona mata asiri.

Ganin ta shiga hannun hukuma sai ta yi kira ga duk masu irin wannan aiki su daina, domin ba abin yi ba ne. Ta ce ba zai kai su ko’ina ba sai hallaka, inda ta kara da cewa ita ma yanzu ta shiga da-na-sani.

A bangaren saurayin Hadiza, Bala Shu’aibu, mai shekara 21, wanda ya hada kai da ita wajen yin garkuwa da yarinyar,  majiyarmu ta ce ya taso ne daga garin Lafiyar Lamurde da niyyar aikata hakan. Ya kuma ce suna zaune ne kawai suka shirye sace yarinyar da nufin a ba su kudi.

Da yake amsa tambaya ko yana da iyayen gidan da suke sa shi wannan aikin, sai ya ce ba ya da ubangida, shi da Hadiza budurwarsa ne kawai suka aikata hakan, kuma bayan sun yi nasara suka je suka ajiye yarinyar a wani otel da ke Unguwar Na-yi-nawa, inda a can ne ’yan sanda suka kama su.

Ya ce ko belinsa aka bayar yanzu ba wanda zai tsaya masa, domin daga Lafiyar Lamurde ya zo, bai san kowa ba a Gombe.

Da yake bayanin yadda aka sace ’yar tasa, mahaifin A’isha Alhaji Muhammad Modibbo Sarkin Fulanin Pindiga, ya ce da safiyar ranar Litinin ya kai su makaranta a Gombe High School, bayan an tashe su sai Hadiza Babayo ’yar yayansa ta je ta dauke ta daga makarantar, ba tare da sanin kowa ba. Ashe lokacin da ta dauke ta, yayan yarinyar dan shekara bakwai ya gan ta, domin ta sanya nikabi ne lokacin da ta shiga makarantar; shi kuma ya gane ta.

Bayan yaron ya isa gida ne yana kuka,  ya shaida wa mahaifinsa cewa “Baba, Hadiza ta je makaranta ta dauke A’isha ta gudu da ita.” Sai nan take suka tafi makarantar, shi da wani abokinsa suka gaya musu abin da ya faru. Sai suka kira dan sanda da wani ma’aikacinsu, suka kai rahoto ofishin ’yan sanda na Unguwar Pantami.

Alhaji Modibbo ya ce kafin su bar makarantar ya kira yayansa, mahaifin Hadiza, ya tambaye shi cewa ina take, sai ya ce masa tana Gombe gidan gwaggwonta, a Yamma da Tumfure. Sai ya tambaye shi kwanansa nawa rabonsa da ita, inda ya ce masa kwana 17.  Shi ne ya sanar da shi cewa ta je makarantar da ’ya’yansa suke karatu ta sace masa ’ya, A’isha kuma an gan ta.

A cewarsa, sai ya sake tambayarsa a wace ce gwaggwon tata? Ya ba shi lambarta, inda ya yi ta kiran wayar amma ba ta shiga ba. Shi ne jin hakan mahaifin Hadizar ya bar Lafiyar Lamurden ya taho Gombe da kansa.

Sarkin Fulanin ya ce yana zuwa Gombe sai ya kira shi ya ce su hadu a gidan mamarsu. Ashe da ya zo gidan da Hadiza take sai ya tambaye ta aka ce ta fita ba ta dawo ba. Yana tsaye can sai ga ta ta shigo, ya tambaye ta ina ta je? Ta ce ta je gidan yayanta ne sai ya ce su je su gai da kakarsu, wato mahaifiyar babanta. Sai ya dawo da ita sai ta bi shi da wata kawarta. Daga nan ne ya kira shi Sarkin Fulanin ya ce sun zo gidan mamarsu. Ya ce da ya je ya same su sai suka tafi da dan sanda da abokinsa.

Alhaji Modibbo ya kara da cewa suna shiga gidan sai ya ce da yayan nasa, “Dama na gaya maka cewa Hadiza ta sace min ’yata a makaranta.” Sai ya ce shi ya sa ya zo ya nemo ta, ya kuma ce ya nemo ’yan sanda aka tafi ofishinsu, aka matsa ta amma ta ki fadin gaskiya.

Ya ce da ta ji wuya ne ta ce za ta fada. Sai wani a wajen ya ce mata “Hadiza shekarunki sun yi kadan, ba za ki iya aikata haka ba, sai dai idan wadansu ne suka sa ki.”

Ta amsa da cewa sanya ta aka yi kuma za ta fadi inda A’isha take.

Sarkin Fulanin Pindiga ya ce bayan sun koma gefe da wani ma’aikaci ne ta ce gaskiya ita ta sace yarinyar ta mika wa wadansu mutum bakwai a cikin mota kirar Siyana. Aka tambaye ta mutane kuma ta ce ba ta san su ba, ta ji dai sunan wani a cikinsu ana kiransa John.

Da ake tambayarta me ya sa ta dauke yarinyar ta bai wa wadanda ba ta san su ba, ta ce sun kira ta ce a waya suka ce ta sato yarinya ta kawo musu ko su kashe ta; shi ya sa ta dauke kanwarta.

Ya ce daga nan ne aka rika bin diddigi har ta tabbatar da cewa yarinyar tana wajen saurayinta a wani otel a Unguwar Na-yi-nawa, ya kuma ce mutanen sun kira shi sun tambaye shi yana son ’yarsa ko ba ya sonta, idan yana sonta ya kawo Naira miliyan shida ko su kashe ta.

Ya ce sai ya ce musu ya ji zai kawo, suka yi masa gargadin idan ya gaya wa ’yan sanda, wai sun san innarsa da yayansa da inda gidansa yake, za su kashe su.

A cewarsa, sun gaya masa cewa tunda yana son ’yarsa ya kawo Naira miliyan shida washegari Talata, idan kuma bai kawo ba za su kashe ta. Shi ne ya ce musu zai kawo.

Ana wannan tattaunawa ce sai ita Hadiza ta bayyana inda suke ajiye da yarinyar, inda Bala Shu’aibu yake a otel din tare da A’isha.

Mahaifin yarinyar ya tabbatar da cewa Hadiza ta yi ta fakon yarinyar a makaranta sau uku lokacin ana hutu. A ranar da aka koma hutu ne ta yi nasarar dauke ta.

Ya kara da cewa Hadiza takan zo gidansa ta yi kwanaki ta koma. A nan ne har yaran suka saba da ita a matsayin gwaggwonsu, amma ita a Lafiyar Lamurde take zaune da iyayenta, tana zuwa Gombe tana komawa. “Babanta ne ya ce ta dawo Gombe saboda akwai saurayin da yake nemanta a can garinsu kuma ya ce bai yarda da shi ba saboda ana zargin yana shaye-shaye; shi ne dalilin dawowarta Gombe kuma ba a gidana  take zaune dindindin ba,” inji shi.

Jami’ar Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan sandan Jihar Gombe, DSP Mary Malum, ta shaida wa manema labari lokacin da aka gabatar da wadanda ake zargin  cewa suna ci gaba da bincike; kuma idan suka kammala za su kai su kotu don yi musu hukunci.

More Stories