✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Dalilin da Najeriya za ta mallaki hannun jari a Matatar Dangote’

Dabarun kasuwanci ne da a karshe kasar nan za ta ci moriya.

Kamfanin Man Fetur na Najeriya NNPC, ya sanar da matakin da ya dauka na mallakar kaso 20 cikin 100 daga Matatar Man Fetur ta Dangote.

Manajan Darakta na NNPC, Mele Kolo Kyari, ya ce hannun jarin Dala biliyan 2.76 da za su zuba a Matatar Dangote wata manufa ce ta dabarun kasuwanci da a karshe kasar nan za ta ci moriya.

Kyari ya shaida hakan ne a ranar Laraba yayin wani zaman tattaunawa kan al’amuran da suka shafi kudaden da Kamfanin zai batar daga 2022 zuwa 2024 wanda Kwamitin Majalisar Wakilai kan kudi ya shirya.

A cewarsa, “hukuncin da muka yanke na mallakar wani kaso daga Matatar Dangote ya ta’allaka ne da dabarun kasuwanci da kuma hangen nesa.

Kyari ya ce babu wata kasa a fadin duniya da ke dogaro kan albarkatun man fetur irin Najeriya, saboda haka wannan wata dama ce da babu kasar da za ta bari ta subuce mata.

Kazalika, Kyari ya ce ya umarci a binciki zargin sayar wa Najeriya lita miliyan 103 na man fetur a kullum a watan Mayu.

Kwamitin Majalisar Wakilan wanda a yanzu haka ke sauraron bayanai kan kudaden da kamfanin zai kashe tsakanin 2022 zuwa 2024, ya bukaci a gudanar da bincike kan zargin sayar da litar mai miliyan 103 a kullum.

A lokacin da yake amsa tambayar Kwamitin kan sayarwa ’yan Najeriyar lita 103 na man fetur a kullum, Kyari ya ce za su binciki gaskiyar zancen.

Ya kuma shaida cewa, idan akwai ranar da ake saye ko shan lita miliyan 103 na fetur, bai sani ba.

Amma ya diga ayar tambaya lokacin da aka gabatar masa da wadannan alkaluma.

Ya ce babu shakka shi ya shaida hakan kwanaki uku da suka gabata, amma ya ce za su bincika.

Matatar Dangote ta Dala biliyan 15 da ake dab da kammala ta a Legas ana sa ran za ta rika tace litar man fetur miliyan 50 a kullum.

Majalisar Zartarwa ta amince a mallaki hannun jari

Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince wa Gwamnatin Tarayya ta sayi kashi 20 cikin 100 na hannun jarin Matatar Mai ta Dangote a kan Dala biliyan 2.76.

Minista a Ma’akaitar Mai, Timipre Sylva ne ya sanar da haka bayan taron Majalisar da aka gudanar tun a farko watan Agusta.

Aminiya ta gano cewa kudin hannun jarin da gwamnatin za ta saya a Matatar Man Dangoten ya kusa ninka abin da gwamatin za ta kashe a wurin gyaran matatun mai na Kaduna da Warri.

Sylva ya ce Majalisar Zartarwar ta amince a kashe Dala biliyan 1.48 domin gyaran matatar mai da ke Kaduna da kuma Warri.

Gyaran matatar mai da ke Kaduna zai lakume Dala miliyan 586.9, na Warri kuma Dala miliyan 897.7, kuma an kasa yadda za a gudanar da aikin zuwa gida uku.

“Kashin farko za a kammala a cikin wata 21, na biyu kuma a cikin wata 23, sai kashi na uku da za a kammala gayan a wata 33,” inji ministan, wanda ya ce an bayar da aikin ne ga kamfanonin Messrs Saipem SPA da kuma Saipem Contracting Limited.

Game da aikin gyaran Matatar Mai ta Fatakwal da a aka bayar tun da farko, Sylva ya ce ’yan kwangilar sun riga sun fara aiki bayan sun karbi kafin alkalami.

“An fara aikin gyaran Matatar Mai ta Fatakwal bayan an ba ’yan kwangilar kashi 15 cikin 100 na kudin aikin.

“Zaman namu ya kuma amince a rika bayar da bayanai daga lokaci zuwa lokaci, saboda haka nan gaba za mu je rangadi a matatar tare da ku,” a cewarsa ga manema labarai bayan taron.

A watan Maris ne Majalisar Zartarwar ta amince da kashe Dala biliyan 1.5 domin gyaran matatar, wadda ita ce mafi girma a Najeriya.

Kudaden shigan Kamfanin NNPC da kasafin kudi da kuma rance da bankin Afreximbank ne dai ake amfani da su wajen gyaran matatar.