✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da nake neman na kaina duk da arzikin mahaifina —Yayar Davido

Ni wannan ita ce akida ta kuma ina fatan kowa zai yi koyi da ita.

Sharon Ademefun, diyar hamsakin attajirin nan, Adedeji Adeleke kuma ’yar uwar fitaccen mawakin Afrobeats na Najeriya, Davido, ta bayyana dalilin da take neman na kanta duk da arzikin mahafinta.

Cikin wani hoton bidiyo da ya karade dandalin sada zumunta na Instagram, Sharon ta ce da yawan mutane suna mamakin yadda take kwadago wajen neman na kanta duk da tarin dukiya da mahaifinta ya tara.

Ta ce dukiyar mahaifinta ba ta sa ta taba jin sha’awar ta daina neman na kanta ba.

Sharon ta bayyana yadda ta taso cikin ’ya’yan hamshakan masu kudi a Birtaniya, amma duk da haka suke fadi-tashin neman na kansu, lamarin da ta ce shi ya kara mata kwarin gwiwar ita ma ta fita ta nema da kanta.

A cewarta, “mutane da dama sun sha zuwa su tambaye ni kan dalilin da nake aiki?

“Kawai saboda na yi digiri har na biyu kuma mahaifina yana da dukiya sai na zauna ba tare da na nemi na kaina ba?

“Na yi karatu a makarantu da ’ya’yan attajirai da ’yan gidan sarauta a Birtaniya, amma duk cikinsu babu wanda ba shi da zuciyar neman na kansa.

“Ba sa taba daukar kawunansu a matsayin masu kudi.

“Ba sa taba jin cewa saboda a yau sun fito daga gidan kudi su zauna komai sai dai a yi musu ba, kullum daukar kawunansu suke yi a matsayin talakawa da dole su ma su tashi su nemi na kansu.

“To irin wannan dabi’a gaskiya a nan nima na koya, kuma ina farin ciki sosai a kan hakan.

“Tabbas ina godiya marar misali ga mahaifina da babu shakka ya yi min duk wani abu a rayuwa har zuwa minzali shagwaba ni da duk wasu abubuwan jin dadi da attajira ke yi wa ’ya’yansu.

“Sai dai wannan jin dadi bai sa na gaza fahimtar cewa a rayuwa ya kamata mutum a ce yana da zuciyar neman na kansa kuma na koyi tattalin duk wata dukiya da na samu.

“Don iyayenka suna da arziki, ba ya nufin kai ma mai arziki ne.

“Galibi ’ya’yan masu kudi sukan zauna su rika rayuwa tamkar su ne masu kudi, sai dai ba su san yadda ake alkinta wannan dukiya ba.

“Ina so ’ya’ya su ji dadi su more rayuwa kamar yadda nima nake yi, amma kafin hakan ya tabbata, dole sai nima na tashi na nemi na kaina ka’in da na’in kamar yadda shi ma mahaifina ya mike tsaye wurjanjan ya nemi na kansa har ya zama abin da ya zama.

“Saboda haka ni wannan ita ce akida ta kuma ina fatan kowa zai yi koyi da ita.

Sharon Ademefun yaya ce a wurin mawaki Davido, kuma ita ce mai Kamfanin Rona Wigs Studio, daya daga cikin shahararrun masu sayar da gashi.

Tana auren wani dan kasuwa mai suna Yomi Ademefun, kuma Allah Ya albarkaci aurensu da ’ya’ya uku a yanzu haka.