✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalilin da PDP ta lallasa APC a zaben Kananan Hukumomin Abuja

Jam'iyyar Buhari ta APC ta sha kaye a Karamar Hukumar Cikin Birni.

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta yi wa jam’iyyar APC mai mulki a kasar wankin babban bargo a zaben Kananan Hukumomin Abuja da ya gudana a ranar Asabar.

Daga cikin Kananan Hukumomin da PDP ta samu nasara har da Karamar Hukumar Cikin Birni ta AMAC (Abuja Municipal Arewa Council, wadda ta kasance cibiyar da ta yi wa Fadar Gwamnatin Najeriya tushe mai mulki a karkashin inuwar jam’iyyar APC.

Aminiya ta ruwaito cewa, baya ga samun nasara a Karamar Hukumar da ta yi wa Shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC masaukin baki, PDP ta kuma lallasa jam’iyyar mai ci a Kananan Hukumomi 10 daga cikin 12.

A bisa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, Shugaba Buhari shi ne ke zaman gwamnan Abuja tare da wasu ministoci biyu da ke gudanar da mulki a madadinsa, sai dai hakan bai sa PDP ta ragawa jam’iyyarsu ba.

A sakamakon Kananan Hukumomin da Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta sanar, Christopher Zakka wanda ake yi wa lakabi da Maikalangu na jam’iyyar PDP, ya samu kuri’u 19,302, inda ya lallasa abokin takararsa na jam’iyyar APC, Mista Murtala Usman Karshi (Yamarayi) wanda ya samu kuri’u 13,249 a Karamar Hukumar ta Cikin Birni.

Duk da cewa APC ce ta yi nasara a rumfar zaben da ke Fadar Gwamnatin Najeriya ta Villa, sai dai masu ruwa da tsaki sun alakanta rashin nasarar da ta yi a Karamar Hukumar da rikicin cikin gida da ya mamaye jamiyyar.

Wani jigo na jam’iyyar APC a yankin ya shaida wa Aminiya cewa, rashin amincewa da dan takara daya da za a goyi baya ne ya haddasa wa jam’iyyar faduwa a zaben.

Ana iya tuna cewa, a ranar Alhamis ta makon jiya ce Kotun Koli ta ayyana Mista Karshi a matsayin gwanin takara na jam’iyyar APC, a yayin da Suleiman Alhassan Gwagwa shi ma ya rika ayyana kansa a matsayin dan takarar da jam’iyyar ta tsayar a zaben Karamar Hukumar ta Cikin Birni AMAC.

A Karamar Hukumar Bwari, John Gabaya na jam’iyyar PDP da ya samu kuri’u 13,045 ne ya lallasa Audi Shekwolo na jam’iyyar APC mai kuri’u 7,697 kacal.

Ita kuwa Karamar Hukumar Kuje, dan takarar jam’iyyar PDP, Abdullahi Suleiman Sabo wanda ya samu kuri’u 13,301 ya doke abokin takararsa na jam’iyyar APC Sarki Hamidu Gaube wanda ya samu kuri’u 7,694.

Sai kuma Karamar Hukumar Gwagwalada, inda Alhaji Abubakar Jibrin Giri na jam’iyyar APC da ya samu kuri’u 11,125, ya lallasa abokin hamayyarsa na jami’yyar PDP, Mohammed Kassim Ikwa mai kuri’u 9,597.

Dandali Chiya na jam’iyyar APC ne ya samu galaba kan abokin takararsa na jamiyyar PDP, Haruna Pai a zaben Karamar Hukumar Kwali.

Baturen Zaben na Karamar Hukumar Kwali, Wesley Daniel, ya sanar cewa Misya Chiya ya samu kuri’u 7,646 yayin da kuma Mista Pai ya samu kuri’u 7,345, wanda tazarar da ke tsakaninsu ba ta wuce ta kuri’u 301 ba.

A Karamar Hukumar Abaji kuma, kuri’u 7,289 Alhaji Yahaya Garba Gawu na jam’iyyar PDP ya samu, inda mai bi masa ya samu kuri’u 4,062.

Sai dai wakilinmu ya ruwaito cewa, a yanzu lamarin zaben Karamar Hukumar ta Abaji ya koma gaban Kotun Koli wacce ita ce ke da hurumin tantance zare da abawa a tsakani.