✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalilin da sojoji fiye da 200 za su ajiye aiki —Nwachukwu

Rundunar sojin ta yi watsi da zargin cin hanci da rashawa na daga cikin dalilan da suka sanya sojojin ajiye aikin.

Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta magantu kan rahotannin da suka ce yanzu haka sojoji sama da 200 sun mika takardunsu na ajiye aiki domin tube kakinsu.

Kakakin rundunar sojin Najeriya, Birgediya Janar Onyeama Nwachukwu ya tabbatar da wannan labari na shirin barin aikin wasu daga cikin sojojin kasar.

A sanarwar da ya raba wa manema labarai ranar Asabar, ya ce sojoji 243 ne suka gabatar da takardun barin aikin ga Babban Hafsan Sojan Kasa, Laftanar-Janar Faruk Yahya.

A cewarsa, sojojin sun gabatar da bukatar ajiye aikin ce a bisa ra’ayi na kashin kansu, wanda ba shi ne farau ba kuma yana faruwa a kowacce ma’aikata muddin ya yi daidai da tsare-tsarenta.

Sai dai Nwachukwu ya yi watsi da zargin cewar cin hanci da rashawa da rashin ingantattun kayan aiki na daga cikin dalilan da suka sanya sojojin gabatar da bukatar ajiye aikin.

Kakakin ya bayyana cewa, “irin wannan rahotan na bata suna na taimakawa wajen karya gwiwar sojojin da ke bakin daga, su na sadaukar da rayukansu domin kare Najeriya.”

Nwachukwu ya ce gwamnatin Najeriya ta samar da kayan aiki na zamani ga sojojin da su ke yaki da ’yan ta’adda, yayin da kuma ake biyansu kudaden alawus akan kari saboda aikin da su ke wanda tuni aka fara ganin nasarar sa.

A karshe sanarwar ta ce shugaban rundunar sojin Janar Yahya ya gode wa sojojin da za su ajiye aikin akan gudummawar da suka bayar, tare da musu fatan alheri.

Barin aikin sojojin na zuwa yayin da Najeriya ke tsakiyar yaki da ’yan ta’addan Boko Haram da ’yan bindigar da suka hana jama’ar kasar zaman lafiya.

Bayanai sun ce wadannan zaratan sojoji da suka gabatar da bukatar tube kakinsu, akasarin su kanana ne wadanda su ke bakin daga wajen fafatawa da ’yan ta’addan da ke kawo zagon kasa ga zaman lafiyar kasar.