✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda bunkasar tattalin arziki zai shafi talaka a Najeriya —Farfesa Darma

Duk bunkasar tattalin arziki, tasirinsa zai zama ragagge matukar ba a samu sauki a farashin kayan abinci ba.

A makon da ya gabata ne Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar da wani rahoton da ya bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya ya bunkasa da kashi 3.98 cikin 100.

Domin sanin wadanne tsare-tsare gwamnatin tarayya ta yi wajen cimma wannan nasara, Aminiya ta tattauna da Farfesa Nazifi Abdullahi Darma, masani a kan harkar da ya shafi Tsimi da Tattalin Arziki.

Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Me za ka ce game da sabon rahoton da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS), ta fitar a kan bunkasar tattalin arzikin Najeriya?

Wato wannan kididdiga da gwamnatin tarayya ta fitar wato na ci gaban tattalin arzikin kasa da aka samu na kashi 3.98 cikin 100, ya nuna cewa wato tattalin arzikin ya samu bunkasa fiye da inda aka zata, duk da cewa tattalin arzikin ya samu gibi ko kuma mashasshara har sau biyu a cikin shekara hudu da suka wuce.

Wannan kuma ya nuna cewa mutanen Najeriya alhamdulilah mutane ne masu aiki da kwazo, kuma masu tashi tsaye a kan dukkan matsaloli da ya shafe su za su iya kokari su yi maganin wannan.

Ta wani bangaren kuma za a iya cewa tsare-tsaren tattalin arzikin da gwamnati ta yi, sun yi tasiri wajen cimma wannan nasarar.

Mene ne GDP a Hausance? Ta yaya mutane za su fahimce shi?

To shi idan aka ce GDP a turance ana nufin ‘Gross Domestic Products’ kuma wannan ya na nuna cewa jimillar tattalin arziki na kasa an auna shi a wani lokaci, yawanci kuma ana auna shi ne bayan dukkan wata uku sannan sai a kididdige wadannan wata ukun a hade sai a samu ainihin bunkasar tattalin arziki da aka samu a cikin shekara guda, to wannan a Hausance shi ne abin da ake kira ma’auni na auna arzikin kasa.

Wani lokaci za ka ga ma’aunin ya samu ci gaba idan tsare-tsare tattalin arzikin sun yi nasara, a wani lokacin kuma za ka ga ma’aunin ya samu ci baya idan tsare-tsaren tattalin arziki na gwamnati ba su samu nasara ba, ko kuma aka samu wata annoba ko wata musiba, sai ka ga cewa wato ma’aunin tattalin arzikin ya yi kasa.

Wadanne muhimman abubuwa rahoton ya kunsa?

Shi dai wannan rahoto ya kunshi muhimman abubuwa kamar haka; na farko wato gaba daya tattalin arzikin ya nuna cewa, bangaren man fetur da gas wanda ana ganin kamar shi ya fi kowanne tasiri, gaba daya bai kai kashi shida na tattalin arzikin ba.

Saboda haka da ba na man fetur ba da ake kira ‘non oil sector’ shi ne ya ke ya bada kusan kashi 95 na gaba daya karfin tattalin arzikin. To, kuma wannan ya na nuna cewa idan aka yi tsare-tsare masu kyau kuma masu tasiri duk da gashi yanzu ana tunanin wato daina amfani da man fetur a koma amfani da wasu hanyoyi na makamashi, to lallai tattalin arzikinmu zai iya ci gaba da samun bunkasa da kuma zama da karfinsa ko da an daina samun cinikin man fetur kamar yadda ake yi.

Rahoton ya ce tattalin arzikin ya bunkasa da kashi 3.98 cikin 100. Me hakan ya ke nufi?

To wannan rahoto ya nuna cewa an samu kashi uku da ‘yan kai na bunkasar tattalin arziki, wato wannan ya na nuna cewa bangarori da yawa kusan 30 da ‘yan kai na tattalin arziki na kasar, kowane ya ba da gudunmawa wajen samun wannan ci gaban alkaluma da aka yi.

To, amma muhimman bangarori guda biyar wadanda su ne suka fi kowane ba da gudunmawa da tasiri wajen wannan ci gaba, su ne bangaren noma, bangaren zirga-zirga, bangaren cinikin cikin gida, bangaren masana’antu da kuma bangaren da ya shafi gine-gine.

To ka ga wannan ya na nuna cewa nan gaba duk wani tsari na tattalin arziki da gwamnati za ta yi, ya kamata ta yi amfani da wadannan bangarori wadanda suka fi ba da tasiri a ga cewa tsare-tsaren da za a yi, ya zama cewar an taimaka wa wadannan bangarori domin su ne suka fi ba da gudunmawa da nasara a ci gaban tattalin arziki.

To kuma babban abin da ya kamata mu kula shi ne; yanzu da ake da matsala ta rashin zaman lafiya da tsaro a Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas, amma duk da haka bangaren noma ya ba da sama da kashi 24 na gaba daya tattalin arzikin kasar, don haka yana nuna cewar idan da akwai zaman lafiya da nutsuwa da kwanciyar hankali, mai yiwuwa tasirin da za a samu na bunkasar tattalin arzikin, sai ya rubanya na yanzu.

Ta yaya hakan zai shafi rayuwar talaka kai-tsaye?

Wannan alkaluma da Gwamnatin Tarayya ta fitar zai iya shafar tattalin arziki da kuma rayuwar talaka, idan har wannan ci gaba na tattalin arziki ya samar sauki da raguwar farashi na abubuwa a rayuwa.

Ka ga gaskiya abin da ke faruwa akasin haka ne yanzu, domin idan aka kula za a ga cewar mafi yawancin abin da ya fi damun jama’a a yanzu shi ne tashin farashin kayan abinci kuma abincin nan shi ne muhimmin babban abu a rayuwar mutane domin kusan dukkan magidanta suna kashe misalin kashi 55 zuwa 56 na duk abin da su ke samu wajen cin abinci.

To duk wani tattalin arziki da za a samu da bunkasarsa, tasirinsa zai zama ragagge matukar ba a samu sauki a farashin kayan abinci ba, wanda jama’a su ke kashewa da kudadensu ba, illa iyaka gwamnati ta duba ta ga wane tsare-tsare ya kamata a yi domin a samu sauki a tashin farashin kayayyakin nan, musamman dai shi bangaren abinci wanda mun san cewa wasu kasashe suna da tsare-tsare wanda gwamnati ta ke yi don idan farashin ya tashi, ya haura wani mizani, domin idan farashin abincin ya yi matukar sauka shi kuma manomi ba zai iya samun karfin giuwa ya yi noma ba.

Sannan idan ya tashi ya yi yawa, shi kuma talaka da ba ya noma ya shiga cikin damuwa, sai dai an zo matsaikacin matsayi, inda shi mai noma ba a hana shi yin noma ba saboda farashi ya yi kasa, shi kuma mai siya farashin bai yi tsada ba.