✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin rashin tsaro a Gwamnatin Buhari —Kwande

Ya tunantar da Gwamnatin Shugaba Buhari cewa mutane take mulka ba dabbobi ba

Daya daga cikin ’yan Kungiyar Dattawan Arewa, Alhaji Yahaya Kwande, ya ce gazawar Gwamnatin Shugaba Buhari ce ummulhaba’isin da ya sa matsalolin tsaro suka yi wa Najeiya dabaibayi.

Kwande wanda ya zanta da wakilin Aminiya a birnin Jos ya ce, “Gwamnatin Buhari ta gaza kuma ta faru ta kare domin kuwa kasar nan ta gama kenan.”

A yayin da ayyukan ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane ke kara ta’azzara kullum musamman a kauyuka inda rayuka da dama sun salwanta, Kwande ya ce, ’yan bindiga da masu garkuwa suna yi wa mutane kisan ganin dama a lokaci da kuma yadda suke so.

“Harkar tsaro a kasar nan ta tabarbare kuma Allah Ne kadai Ya san abin da ke faruwa a kauyukan kasar nan wanda a kullum muna rayuwa cikin fargaba da tsoro mai tsananin gaske.”

Ya ce mutanen birnin da na kauye a wannan zamani ba su da wani sukuni, don hatta baki sun zama barazana ga mutane a gidajensu yayin da suka nufaci kai ziyara.

A cewar Kwande, rashin baiwa tsaro muhimmanci da Gwamnatin Buhari ta yi tun ‘fil azal’ ya yi tasiri wajen jefa kasar cikin halin da ta tsinci kanta a yanzu.

Ya kara da cewa, rashin jajircewa da halin ko in kula da gwamnatin ta nuna gami da kwadayi da son zuciya, sun taka rawar gani wajen bai wa matsalar tsaro gudunmuwa mai girman gaske a kasar.

Kwande wanda ya tunantar da gwamnatin cewa mutane take mulka ba dabbobi ba, ya yi kira da a yi wa harkar tsaro karatun ta nutsu kuma gwamnati ta jingine duk wasu ayyukanta ta mayar da hankali wajen inganta al’amuran da suka shafi tsare rayuka da dukiyoyin al’umma wanda shi ne nauyi na farko da rataya a wuyanta.

Sai dai ya ce har yanzu ba a makara ba don ana iya samun aminci a kasar amma dole sai gwamnati ta koma kan taswirarta ta tsare-tsare domin ganin abin da zai faranta wa jamai’an tsaro kuma dole ne ta hada kai da ’yan adawarta domin tabbatar da zaman lafiya don don gwamnati kadai ba za ta iya wannan aiki ba.