✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa ba za a janye wa Mali takunkumi ba – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce har yanzu akwai wasu al’amura da ke bukatar a shawo kansu dangane da shirin sojin Mali na danka wa farar…

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce har yanzu akwai wasu al’amura da ke bukatar a shawo kansu dangane da shirin sojin Mali na danka wa farar hula mulkin kasar gabanin Kungiyar ECOWAS ta Kasashen Yammacin Afirka ta janye takunkumin da ta sanya wa kasar.

Fadar Shugaban na Najeriya ta sanar cewa da yiwuwar shugabannin Kasashen ECOWAS su sake zama domin tattaunawa kan rikicin siyasa da ya ki ya ki cinyewa a makociyar kasar.

A wani rahoton da jaridar BBC ta wallafa, sanarwar da fadar Buhari ta zo ne bayan ya gana da tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan wanda ya kasance jakadan ECOWAS na musamman.

A cewar sanarwar, “wakili na musamman ya ce shugabannin sojin har yanzu ba su cika sharudan ECOWAS ban a nada farar hula a matsayin Mataimakin Shugaban Kasa.”

Kungiyar ECOWAS ta kakaba wa Mali takunkumi ne bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa Shugaba Ibrahim Boubacar Keita a watan Agustan da ya gabata.

A baya bayan ne aka nada tsohon Ministan Tsaro Bah Ndaw, a matsayin shugaban rikon kwarya a Mali wanda zai jagoranci shirya zaben da za a mika wa farar hula mulkin kasar.