✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa Buhari zai dauki ma’aikata 774,000

Hukumar Kula da Aiki (NDE) ta ce Shugaba Buhari ya bullo da shirin daukar ma’aikata 774,000 ne domin cimma wasu manufofi bakwai. Shugaban NDE Nasiru…

Hukumar Kula da Aiki (NDE) ta ce Shugaba Buhari ya bullo da shirin daukar ma’aikata 774,000 ne domin cimma wasu manufofi bakwai.

Shugaban NDE Nasiru Ladan, wanda ke jagorantar kwamitocin tantance wadanda za da dauka aikin daga jihohi ya bayyana haka a zantawarsa da Aminiya.

Za a dauki kananan ma’aikatan wucin gadi 774,000 ta hanyar daukar mutum 1,000 daga kowacce daga kananan hukumomin Najeriya 774. Za su yi akin na SWP ne na tsawon wata uku.

Ya ce bayan gwaji a wasu jihohi takwas ne Shugaba Buhari ya fadada shirin zuwa kasa baki daya.

Manufofin shirin:

Ya ce daga cikin manufofin shirin akwai bunkasa yanayin samun masu karamin karfi.

“Ka yi tunanin amfanin da za a samu idan aka ba da Biliyan N52 a Kananan Hukumomi ta bangaren karuwar kudaden da mutane ke samu da tasirinsu ga tattalin arziki”.

Shirin zai kuma samar da ayyukan yi ga mutane a yankunansu wanda zai rage kaura daga kauyuka zuwa birane.

Sannan zai nuna wa mutane amfanin zaman lafiya da juna da kuma muhimmancin dogaro da kai.

Da shirin, marasa aiki za su koyi yadda za su lallaba abun da suka samu domin yin wasu harkokin neman kudui.

Ana kuma kokarin ganin shirin ya taimaka wajen lura da abubuwan da ke faruwa a cikin al’umma.

Akwai kuma koarin ganin shirin ya dore. “Ba za mu ci gaba ba sai idan mun ci gaba da abun da muka fara; abun da muke shirin yi ke nan”, inji shi.

Ya ce bayan kammala aikin na wata uku, za a yi amfani da sakamakon binciken za a gudamar domin daukar matasa aikin gona.

A cewarsa SPW shi ne shirin daukar ma’aikata mafi girma a Najeriya kuma NDE mai alhakin aiwatar da shi, ba za ta bari a yi murda-murda ba.

“Mutane sun dauka za su iya juya abubuwa, amma ba su san abun da ya kunsa ba kamekame kawai suke yi. Aikin Gwamnatin Tarayya ne kuma ba za mu ba da kunya ba, inji shi.

Ana iya tunawa Majalisar Tarayya ta dakatar da daukar ma’aikatan bayan cacar baki tsakaninta da Minista a Ma’aikatar Kwadago, Festus Keyamo da Kwamitinta kan kwadago.

Daga baya Shugaban Kasa ya ba Kayamo izinin ci gaba da aikin daukar mutanen da za su fara aiki daga watan Oktoba zuwa Disamban 2020.