✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa China ta daina ba Najeriya bashi – Lai Mohammed

Sai dai ya ce Najeriya na duba yiwuwar ciyo bashin daga hanyoyin gida da na ketare.

Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya bayar da dalilan da suka sa kasar China ta daina ba Najeriya bashi.

Aminiya ta rawaito yadda jan kafar da Chinan ke yi wajen ba wa Najeriya bashi ya sa Gwamnatin Tarayya ta fara juya akalar ciyo bashinta zuwa wasu kasashen Turai.

Ya bayyana hakan ne lokacin da ya ziyarci gidan Talabijin na Trust TV ranar Litinin.

A cewar Ministan, “Na tuna yadda Ministan Sufuri yake korafi kan cewa duniya gaba daya na daukar matsayinta ne a kan Najeriya ta hanyar la’akari da abin da ’yan kasar ke fade a kan gwamnatinsu.

“Batun cewa gwamnati na dab da tsiyacewa ina tunanin shi ne ya sa suka ja da baya, shi ne ya sa suka hana mu bashi. Abin da muka yi shi ne muje wasu hanyoyin don samo kudaden daga cikin gida.

“Dalilin da ya sa muka fi na’am da cin bashin China shi ne sharuddansu na da sauki, kuma muna da fahimtar juna da su kan lokacin fara karba da kuma biyan bashin.”

Ministan ya kuma ce amma har yanzu Najeriya ba ta hakura ba, amma tana kuma duba yiwuwar samun basukan daga wasu hanyoyin don kammala wasu manyan ayyuka da suka fara.

“Idan masu baka bashi na da wuyar sha’ani, dole ka nemo wasu hanyoyin samun wasu kudaden. Ba mu yi watsi da ayyukan da muka fara ba saboda haka, aikin titin jirgin kasa na Kano zuwa Kaduna da wani kamfanin kasar Portugal ke yi har yanzu ana ci gaba da yi.

“Gaskiya ne muna samun matsala daga China, amma muna kokarin samun wasu hanyoyin cin bashin daga ciki da wajen Najeriya. Wannan wata ’yar manuniya ce kan yadda gwamnati ta himmatu wajen samar da manyan ayyuka da kuma samar da ayyuka ga ’yan kasa.