✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Dalilin da ya sa Matan Arewa ke fuskantar matsala wajen samun tallafin Gwamnati’

Wata Kungiyar Matan Arewa mai suna Jam’iyyar Matan Arewa (JMA), ta sanar cewa galibi mata a yankin su na fuskantar matsaloli wajen samun tallafin kudi…

Wata Kungiyar Matan Arewa mai suna Jam’iyyar Matan Arewa (JMA), ta sanar cewa galibi mata a yankin su na fuskantar matsaloli wajen samun tallafin kudi na shirye-shirye daban-daban da gwamnati ke aiwatarwa.

Da wannan ne Kungiyar ta ke kiran wakilai daga Bankin Baiwa Manoma Basussuka da Inshorar Noma na NIRSAL, Bankin Guaranty Trust, First Bank da kuma Gwamnatin Jihar Kaduna a kan su bijiro da hanyoyin baiwa Mata samun duk wasu tallafi na Gwamnati da suka biyo ta hannunsu.

Shugabar JMA, Hajiya Rabi Musa Saulawa, ta ce Mata sune ginshiki kuma jigon rayuwar kowace al’umma saboda haka suka fi cancantar bukatar tallafi domin samun iko da madogara ta dawainiya da kula wa da gidajensu.

A cewarta, “Mata su kasance suna fuskantar matsaloli wajen samun tallafi na rance da karbar basussukan Gwamnatin Tarayya da na Jihohi ke bayar wa.”

“Don haka na yanke shawarar tattauna wa da wakilan wasu bankuna, NIRSAL, da Bankunan Kananan Masana’antu na Jihar Kaduna, da Asusun Tallafawa Mata na jihar Kaduna domin su fada mana yada za mu rika samun wannan tallafi.”

Ta kuma ce, “Gwamnatin na iya bullo da wata hanya mafi sauki; wadda ba ta bukatar sai mun yi rajista da Hukumar Kula da Harkokin Kasuwanci (CAC) ko kuma samun Lambar Tabbatar da Asusun ajiya na Banki (BVN) domin matan karkara su samu damar samun tallafin.”