✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da za mu sauya takardun Naira —Buhari

Za a kaddamar da sabbin takardun kudaden ne a ranar 15 ga watan Disamba.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya amince Babban Bankin Najeriya  CBN ya yi sauye-sauyen a wasu daga cikin takardun kudaden kasar.

Buhari ya zayyana dalilan amincewarsa da sauye-sauyen yayin wata hira da ya yi da fitattun ‘yan jarida Halilu Ahmed Getso da Kamaluddeen Sani Shawai da harshen Hausa.

Ya bayyana cewa shirin zai taimakawa kasar a fannoni da dama, kamar yadda wata sanarwa da kakakinsa Malam Garba Shehu ya fitar ta ce.

“Shugaba (Buhari) ya ce dalilan da CBN ya zayyana masa kan bukatar yin sauye-sauyen, za su taimaka wajen rage hauhawar farashin kayayyaki.

“Sannan za su rage jabun kudade da ke yawo a hannun mutane da kuma rage yawan kudade a tsakanin al’umma.

“Mutanen da suka binne haramtattun kudade a karkashin kasa, su ne za su fuskanci kalubale idan muka yi hakan.

“Amma ma’aikata da ‘yan kasuwa da ke samun kudaden shiga ta hanyoyin halal, ba za su fuskanci wata matsala ba,” a cewar Buhari.

Buhari ya kara da cewa, ba ya ganin adadin wata uku da aka diba don gudanar sauye-sauyen ya yi kadan kamar yadda wasu suke fada.

A makon da ya gabata, CBN ya sanar da shirin sauya fasalin wasu daga cikin kudaden kasar na takardu.

Cikin wata sanarwa da bankin ya wallafa a shafukan sada zumunta a karshen makon da ya gabata, ya ce sauye-sauyen za su shafi takardun Naira 1,000, 500, 200 da kuma 100, ba dukkan kudaden kasar ba kamar yadda ake ta yadawa bisa kuskure.

Gwamnan CBN, Godwin Emefiele yayin ganawa da manema labarai ranar Laraba a Abuja, ya ce za a kaddamar da sabbin takardun kudaden ne a ranar 15 ga watan Disamba.

Ministar Kudi ta yi bore

Tuni dai Ministar Kudin Najeriya Zainab Ahmed ta nesanta ma’aikatarta da matakin na CBN tana mai bayyana damuwar cewa a kasa da kwana biyu da sanar da shirin, farashin Dala ya tashi daga N740 zuwa N788.

Ta bayyana cewa sam CBN bai tuntube Ma’aikatar Kudi ba kafin yanke shawarar sauya wasu takardun Naira.

“Amma a matsayina na babbar jami’a a haskar tsare-tsaren kudi a Najeriya, wannan tsarin da ake shirin aiwatarwa na da matukar hadari ga darajar Naira,” a cewarta.