✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin mu rika amfani da kayan lambu a abincinmu na yau da kullum

Suna kuma taimakawa wajen kare kwayoyin halitta daga lalacewa, cutar Kansa da kuma sauran cututtuka.

A lokuta daban-daban, bincike ya nuna cewa mutanen dake yawaita amfani da kayan lambu cikin abincinsu akalla sau biyar a kowacce rana na da karancin barazanar kamuwa da cututtuka da dama, ciki har da sankara da ciwon zuciya.

Yawan amfani da kayan lambu a cikin abinci shine daya daga cikin hanyoyi mafi arha da kuma sauki na kula da lafiya.

Dukkan kayan lambu na kunshe da sinadaran kara lafiya kamar su vitamin, mineral da dai sauransu, ko da yake wasu sun fi shahara wajen irin amfaninsu ga jikin dan Adam. Wasu kayan lambu kan samar da fa’idoji na musamman ga wasu mutanen daidai da bukatun jikin nasu.

Nau’ukan kayan lambun da suka fi kowanne fa’ida da kara lafiya ga jiki sun hada da alayyahu, wake, dankalin turawa, karas, lansir, tafarnuwa, zogale, latas da dai sauransu.

Kungiyar Kula da Lafiyar Zuciya ta Amurka ta bayar da shawarar cin akalla giram 25 na kayan lambu a kullum domin bunkasa lafiyar zuciya.

Yawaita amfani da wadannan nau’ukan kayan a cikin abinci kan taka muhimmiyar rawa wurin taimakawa jiki ya sami saukin sarrafa abinci.

Kazalika, amfani da albasa da sauran dangoginta kamar tafarnuwa na taimakawa sosai wajen kare jiki daga cutar Kansa.

Za a iya amfani da albasa a cikin miyar yauki ko ta dage-dage, ko da yake idan aka yi amfani da danyar albasa ko tafarnuwar sun fi samar da fa’da ta kai tsaye ga jiki.

Bugu da kari, binciken ya nuna cewa akwai nau’ukan kayan lambun dake taimakawa jiki wajen narkar da abinci a kan lokaci. Nau’ukan sun hada da kabeji, gurji, karas, salad da kuma lansir

Galibi dai mutane kan ci wadannan nau’in ganyakan a cikin abinci ko kuma a matsayin abincin su kadai.

Bincike ya kuma nuna cewa cin dankalin turawa na taimakawa masu ciwon suga matuka. Dalili kuwa shine saboda yana kunshe da sinadaran da suke daidaita suga a jikin dan Adam.

A cewar wani bincike da Cibiyar Kula da Cutar Kansa ta Kasa ta fitar, akwai wasu sinadarai da ake kira indoles da isothiocyanates a cikin kayan lambu dake dakile kamuwa da kuma yaduwar cutar Kansa a sassa da daman a jiki, ciki har da mafitsara, mama, saifa da kuma ciki.

Suna kuma taimakawa wajen kare kwayoyin halitta daga lalacewa, cutar Kansa da kuma sauran cututtuka.

Daga www.medicalnewstoday.com