✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin dage wasan Arsenal da Manchester City a Firimiyar Ingila

A ranar Alhamis Gunners za ta karbi bakuncin PSV Eindhoven a gasar Europa.

An dage wasan da ya kamata Arsenal ta karbi bakuncin Manchester City a karawar mako na 12 a gasar Firimiyar Ingila ranar Laraba.

Arsenal wadda ta ci Leeds United 1-0 a makon jiya tana ta daya a kan teburin babbar gasar tamaula ta Ingila mai maki 27.

City mai rike da kofin bara kuwa wadda ta yi rashin nasara da ci 1-0 a hannun Liverpool a Anfield ranar Lahadi, tana ta biyu da tazarar maki hudu tsakaninta da Gunners.

An dai dage wasan da bajiman biyu za su fafata saboda a ranar Alhamis Gunners za ta karbi bakuncin PSV Eindhoven a wasa na biyu na cikin rukuni da ya kamata su buga tun ranar 15 ga watan Satumbar 2022.

Hakan ya biyo bayan zaman makokin rasuwar Sarauniya Elizabeth II.

Arsenal da PSV Eindhoven sun kara sau shida a tsakaninsu a gasar zakarun Turai, inda Gunners ta yi nasara a biyu da canjaras uku, PSV Eindhoven ta ci daya.