✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin dage zaben gwamnoni —INEC

Za a ci gaba da yakin nema zabe zuwa ranar 16 ga watan Maris, 2023

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanar a hukumance, abin da ya sa ta dage zaben gwamnoni da majalisun dokokin jiha zuwa ranar 18 ga watan Maris da muke ciki.

Tun da farko, Aminiya ta wasu majiyoyi a INEC na cewa hukumar ta yanke shawarar dage zaben ne kasancewar lokaci ya kure mata na kwashewa da adana bayanan da ke cikin na’uroroin tantance masu zabe na BVAS kafin zaben da ta tsara gudanarwa ranar Asabar, 11 ga wata.

Daga bisani Kwamishinan INEC na Kasa kan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Festus Okoye, ya fitar da sanarwar cewa, hukumar na bukatar karin lokaci da zai isa ta sabunta bayanan da ke cikin na’urorin BVAS 176,000 da aka yi zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu da su, da ke daukacin kananan hukumomi 774 na Najeriya, gabanin zaben gwamnoni da majalisun dokokin jiha.

Ya ce, “A ranar 3 ga watan Maris, 2023 wasu jam’iyyun siyasa sun garzaya Kotun Sauraron Kararrin Zaben Shugaban Kasa suka izinin bincikar kayan da aka yi amfani da su a zaben, ciki har da BVAS sama da 176,000 da kuma shafin tattara sakamakon zabe na IRev.

“Daga baya INEC ta bayyana wa kotun cewa da wadannan BVAS din za a yi zaben gwamnoni da majalisun dokokin jiha, kuma rashin kayyade lokacin da aka ba masu kara na bincikar kayan zaben na iya kawo wa hukumar tsaiko wajen gudanar da zaben gwamnoni.

“Dalili shi ne akwai lokacin da aka kayyade da za a sanya bayanai a na’urorin BVAS kafin kowane zabe.

“Sannan kasancewar an yi zaben shugaban kasa da su, sai an kwashe, an dana bayanan da ke cikinsu, a sanya musu bayanan da suka dace da zaben gwamnoni da majalisar jiha, sannan a saita musu sabon lokacin da za su fara aiki.

“Duk da cewa kotun ta amince, amma lokaci ya riga ya kure da INEC za ta iya yin wadannan abubuwa kafin zaben; Shi ya sa ba ta da zabi face ta dage zaben zuwa ranar 18 ga watan Maris, 2023,” in ji Okoye.

Ya ce karin lokacin, “ya zama babu makawa, domin tabbatar da cewa an adana duk bayanan zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Maris da ke kan BVAS sama da 176,000 sannan a loda wa na’urorin sabbin bayanai don zaben gwamnoni da majalisun jiha.

“Wannan kuma ba sabon abu ba ne, domin kuwa haka a ake yi a kowane lokacin zabe, hatta a lokacin da ake amfani da na’urar Card Reader,” in ji Festus Okoye.

Ya kara da cewa, dage ranar zaben na nufin, “Za a ci gaba da gudanar da yakin neman zaben har zuwa karfe 12 na dare ranar Alhamis, 16 ga watan Maris, 2023, wato awa 24 kafin ranar zabe.”

Idan ba a manta ba, a ranar Laraba ne dai Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a Abuja ta ba wa INEC izinin fara loda bayanai a kan na’urorin BVAS da za a yi amfani da su a zaben gwamnoni da majalisun jiha.