✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda giyar mulki ta ja wa APC faduwa Zaben Gwamnan Osun

Jigo a APC ya ce lokaci ya kure mata na yin gyara kafin zaben 2023

Wani jigo a Jam’iyyar APC mai mulki ya zarge ta da jawo wa kanta faduwar da ta yi a zaben Gwamnan Jihar Osun na ranar Asabar.

Tsohon dan takarar Gwamnan Jihar Imo a karkashin tutar Jam’iyyar APC a 2019, Uche Nwosu ya ce jam’iyyarsu ce ta ja wa kanta faduwa zaben saboda girman kai da giyar mulki ta sa shugabannin suke ganin ba mai iya ja da su a jihar, suka yi watsi ’yan jam’iyya masu kishi.

Ya bayyana cewa rikicin cikin gida da jam’iyyarsu ke fama da shi a jihar na daga cikin Ummul-aba’isin da ta kasa cin zaben.

Nwosu wanda suruki ne gaba tsohon Gwamnan Jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha, ya ce rashin yi wa ’yan jam’iyya alheri bisa gudunmawar da suka bayar wajen samun nasararta ya sa mambobin APC jihar shantakewa maimakon fitowa haikan don ganin ta sami nasara a zaben.

A ranar Lahadi Aminiya ta kawo rahoton yadda Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanar da Sanata Ademola Adeleke na Jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan Jihar Osun bayan ya kayar da Gwamna Gboyega Oyetola na Jam’iyyar APC.

Da aka tuntube kan haka. Nwosu

ya ce, “APC ta fadi ne saboda yadda suka bari rikicin cikin gida ya ruguza duk tsare-tsarenta a jihar, gami da girman kai, saboda suna ganin idan mulki na a hannunka, sai abin da ka dama.

“APC ta fiye dogaro da karfin mulki, ga shi kwata-kwata ba a kula da ’yan jam’iyya da suka yi mata wahala. Misali shi ne yadda aka yi watsi da iyayen jam’iyar da suka kafa ta don a faranta ran sabbin mambobi.

“Ka dubi yadda suka yi watsi da tsohon gwamnan jihar, Rauf Aregbesola, wanda da shi aka kafa jam’iyyar, saboda suna ganin za su iya yin duk abin da suka ga dama ko babu shi; yanzu ga shi nan ta bare da su.”

Game da ko jam’iyyar za ta iya yunkurawa ta shawo kan matsalolin gabanin zaben 2023, Nwosu ya ce lokaci ya riga ya kure mata na yin sauye-sauyen da suka kamata.