✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Dalilin gaza inganta wutar lantarki daga zamanin Obasanjo zuwa Buhari’

Shirin na PWC shiri ne samar da wutar lantarki bayan 2023.

Dokta Usman Gur Mohammed shi ne tsohon Shugaban Hukumar Kula da Rarraba Wutar Lantarki ta Kasa (TCN), kuma tsohon ma’aikacin Bankin Bunkasa Afirka.

A tattaunawa da gidan talabijin na Trust TV, ya yi bayani kan harkar wutar lantarki da yadda za a samar da wutar isasshiya.

Kuma ya bayyana cewa za a iya samun ci gaba matukar wanda ya samu kujerar Shugaban Kasa ya fahimci harkar da kyau.

Ga yadda tattauanwar ta kasance:

Kana daya daga wadanda aka dora wa alhakin aikin samar da wutar lantarki lamarin da ke da dangantaka da abin da manyan ’yan takarar Shugaban Kasa hudu wato APC da PDP da NNPP da LP suke yakin neman zabe a kai.

Mene ne ra’ayinka a kan wannan?

Shirin na PWC shiri ne samar da wutar lantarki bayan 2023. Mun duba tare da bibbiyar manufofin kowace jam’iyya kafin muka je wannan taro, sannan matsayar da muka cim ma, ita duk da bayanai da alkawuran samar da megawatt 20.000 ko 25,000 babu inda aka yi cikakken bayanin dalili kan yadda muka tsaya cak a megawatt 4,000 a yanzu, kuma babu bayanin yadda za a samar da megawatt 20,000 din.

Babu wani cikakken bayani, hakan ya sa zan iya tabbatar maka cewa manyan jam’iyyun nan hudu ba su fahimci bangaren makamashi ba. Akwai alamar watakila ko sun hau mulki, su ma za su sake yin wasu shekara hudun ne kamar yadda wannan gwamnati ta shekara kusan bakwai ba tare da magance matsalar wutar lantarkin ba.

Amma ba ka tunanin za su ce ba a faye fahimatar yadda abubuwa suke ba har sai mutum ya hau kujera?

Matsalar ita ce harkar wutar lantarki akwai son zuciya a ciki, lamarin da yake sa mutane ba su iya tsayawa su fahimce ta har ma su iya yin wani abu a kai.

Mun tattauna da ’yan kwamitin nan inda muka tsaya a kan cewa za su iya samun Kamfanin KPMG wanda shi ma wani abu ne na idan muka hadu da ni da su muka yi aiki a kai za mu fahimci yadda harkar wutar lantarki take gaba dayanta mu kuma fahimci abubuwan da suka kawo taranaki a harkar, wanda ya sa har yanzu muke a wuri daya ba tare da motsawa ko’ina ba.

Mece ce wahalar da ta janyo har zuwa yanzu wadannan makudan kudin da ake narkawa ba su samar da wutar lantarkin da ake bukata ba?

Bari in fara da lokacin Shugaban Kasa Obasanjo da ’Yar’aduwa da kuma Jonathan.

Zan fada maka abin da ya faru a wadancan lokuta kai har ma da lokacin Buhari.

A lokacin Obasanjo sun yi kokarin yin doka a kan harkar wutar lantarki inda suka mika harkar ga kamfanoni 11.

Ba su yi wani kokarin mayar da harkar ta kasuwanci ba.

Sai dai babban abin da Obasanjo ya yi a lokacinsa shi ne wani aiki ‘Manyan jam’iyyun Najeriya ba su fahimci bangaren ba’ na (NIPP) da muka fara aiki ba tare da cikakken bincike a kai ba.

Kawai dai wasu kamfanonin Turawa sun yi mana bayanin da muka gamsu cewa za su samar mana da bututun iskar gas haka kuma sun sanar da mu cewa ba su za su kakkafa mana kayayyakin ba, don haka za su mika shi ga wani dan Najeriya da ke aiki tare da su wanda zai kula da harkar kakkafa kayayyakin.

Abin da muka yi shi ne kamar kai ne za ka gina gida sai ka ba dan kwangila ya gina maka gidan, sai ya yi maka rufi bayan kuma ba ka fara aikin ginin daga kasa ba. To wannan shi ne kwatankwacin abin da muka yi a NIPP.

Baya ga cewa bincike ya nuna cewa kamata ya yi su tsaya su kula da harkar kasuwancin da kansu.

Kamfanin da ke kula da rarraba wutar da kuma duk wanda zai karba daga hannun kamfanin wanda kuma yake da gogewa a harkar zai nemi a ba shi wasu bayanai da dokokin da suka samar da kamfanonin.

Lokacin da muka fara mun yi asarar kaso 25 amma yayin da muka hau titi don mu nuna abin da muka yi, duka kamfanonin nan sun fada mana haka su ma kamfanonin da suke da kwarewa a kai sun fada mana cewa, “Ku je ku karanta kuma ku samu injiniyoyin da za su bude muku komai a fili.”

Daga baya muka fahimci cewa wanda zai zo wurinmu don haka sai muka takaita yawan takardun karatu domin a bar kamfanonin Najeriya su karba daga gare su.

Wannan ne ya janyo wasu kamfanonin suka mallaki kamfanonin rarraba wutar lantarkin.

Idan muka dauki Shugaba ’Yar’aduwa ya yi wani abu da mutane da yawa ba su yi ba, ya dakatar da harkar canja fasalin wutar lantarkin ya kuma kafa kwamitin da zai binciki harkar sannan ya bayar da shawara, wanan shi ne abin da ya kamata a yi.

Lokacin da Shugaba Jonathan ya zo sai ya ki amfani da wannan rahoto sannan ya dauki matakin sayar da hannun jarin harkar gaba daya.

Sai suka dauko hayar wani dan Indiya wanda ya shawarce su da yin harkar kasuwanci na gwaji a wasu jihohi biyu domin a koyi wani abu kafin a fara harkar kasuwancin gaba daya.

Ko akwai wani amfani da suka kara wa abokan huldarsu, saboda abin da kawai suke hankoro shi ne rarraba mita, ko ba su yi hakan ba?

Abin takaici, hatta kamfanin da yake da dadaddiyar kwarewa idan babu sa ido kan yadda yake gudanar da harkokinsa, za ka iya tafka asara, ta yadda dole a karshe sai ka karbe ragamar tafiyar da shi, ka samu kudi masu tarin yawa fiye da lokacin da ka karbe shi daga mutumin farko. Kwatankwacin abin da ya faru ke nan.

Saboda ba su da kwarewa, ba su da ilimin yarjejeniyar da suka sa hannu a kai da ta ba kamfanonin sahalewa.

Me wannan yarjejeniyar ta kunsa?

Wata yarjejeniya ce da ba ta neman wani katabus daga sauran bangarorin da suka kulla ta.

Ko wannan na cikin dalilan da suka sa kuka kwace kamfanonin kamar na Kaduna (KAEDCO)?

Bari in fada maka abin da ya faru. Mun karfafa gwiwar bankunan Najeriya, saboda wadannan kamfanoni ba su da karfin da za su tara kudaden da ake bukata.

Mun bukaci ’yan Najeriya su zuba jari a harkar kamfanonin rarraba wutar lantarki. Ina nufin gwamnati ta bukaci ’yan Najeriya su zuba jari a harkar kamfanonin.

Kudaden da suka fito daga bankuna na gajeren lokaci ne, kuma suna da dan karen tsada, bai kamata a ce an yi amfani da su wajen samar da kudaden irin wadannan muhimman ayyuka ba.

Mun haddasa matsalar da ta janyo karyewar kamfanonin wutar lantarki, kuma ina tunanin daga nan ne matsalar ta samo asali.

Daga karshe, mun bige da fadawa hannun mutanen da ba su da masaniya ko kwarewa a harkar.

Sai aka wayi gari babu wani ci gaba na ku-zo-ku-gani da aka samu a harkokin kamfanonin.

 A wasu lokuta mukan ji kamfanonin samar da wutar lantarki (GenCos) na ikirarin samar da wasu injina kuma suna samar da karin wutar lantarki…?

Lokacin da nake shugabancin kamfanin, rarraba lantarki ita ce babbar matsalar da muke fama da ita.

Amma abin takaici a yau, mun yi matukar komawa baya ta yadda hatta samar da wutar ma tana nemna gagarar kundila.

Akwai karancin samar da iskar gas, wasu kamfanonin kamar na Shell ma sun janye jikinsu daga rarraba ta, wasu da dama kuma daga cikinsu sun ce ba za su iya mayar da kudaden da suka yi ikirarin kashewa wajen zuba jarinsu ba. Yanzu ga shi a karshe ba ma iya ma samar da megawat 4,000.

Ana ta maganar Mambila musamman a wanan gwamnati sai dai har yanzu ya nuna cewa ba za a iya samar da ita kafin wa’adin gwamnatin b a… Lokacin ina Manajan Daraktan TCN a lokacin da ake ta tarurruka a kan Mambila gaskiya an cire ni, saboda kowa ya san cewa sai na fadi gaskiya.

Ana haka lokacin da Kamafanin China ya turo kwararunsa zuwa Najeriya don sake duba aikin, to su ’yan Bankin China sun lallaba sun zo mun gana inda muka yi magana sosai inda na gano cewa a gaskiya babu wani aiki a kasa.

Idan ka dauki aiki irin wannan abu ne da ke bukatar kudi idan kana da aiki kuma ka kasa samar wa aikin kudi wannan aiki ba zai yiwu ba kuma babu wanda zai sa kudinsa a ciki.

Ban yarda cewa Bankin na China zai sa kudinsa a kan aikin Mambila ba saboda lokacin da muka yi magana da su mun ganmo cewa kudin da za a biya a Mambila shi ne Santi 13 a kan kowane kilowatt na awa daya.

Yaya za mu samu wutar da za mu sayar a kan Santi 13? Wane ne zai sayi wannan wutar ta yaya kuma za mu iya mayar da kudi?

Wannan ita ce tambaya? Ka san mun yi ta surutu a kan Azura wanda shi kuma ya kai Santi 10.4 ko 11 a kan duk kilowatt daya mun yi ta surutu a kai saboda yana da tsada. A wanann maganar mun gano cewa harkar wutar Mambila aba ce mai girma.

Wanann yana nufin cewa ana bukatar ruwa saboda yawan ruwan da ake fitarwa a lokaci guda.

A shekara guda za ka kashe kaso kimanin 20 ko 30 a hakan kuma ruwan ya kare, yana nufin cewa za ka sanya babban janareta.

Idan ka rararba kiyasin abin da za a kashe na sanya janaretan a kan kudin wutar dole ka san kudin wutar zai yi yawa.

Kudin ya kamata ya kasance tsakanin Santi 5 ko 6 a kan kowane kilowatt. Na san cewa aikin ba zai yiwu ba, Bankin Edim na China zai iya yiwuwa yana yaudararmu ne.

Mene ne shirin Gwamnatin Buhari ta fuskar wutar lantarki?

Abin da Buhari ya karba daga Jonathan shi ne an cefanar da harkar gaba daya, sai dai Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki yana karkashin gwamnati wanda kuma aka ba Kamfanin Manitoba Hydro ya kula da shi a madadin gwamnati.

Gwamanti ta karbe abin da ake cewa tsarin tilon mai saye (single buyer model) inda babban dan kasuwa ke saye wutar gaba daya sannan ya sayar wa kamfanonin rarraba wutar lantrarki.

Wannan wani abu ne na samun rangwame?

Eh, wannan wani na samun sauki. Ya kamata ya zama wani abu da za a rika sabunta shi duk bayan shekara biyar, amma yanzu mun yi shekara goma amma har yanzu da shi ake amfani.

A bisa shirin da aka yi Gwamnatin Buhari ta sanya kusan Naira tiriliyan biyu a harkar wutar domin ta dauki nauyin wannan rangwamen sai dai a karshe wannan kudi ba a yi amfani da shi wajen kara yawan megawatt da ake Daga shafi na 2 bayarwa ba, sai dai ana biyan kudin shan wutar. Muna biyan lalacewar harkar wutar.

Saboda me ya sa muke samun daukewar wutar a ko’ina, domin a bara kusan sau 10 ana samun hakan wato National Grid tana faduwa?

Dole ne abin ya lalace domin duk abubuwan da za su hana harkar faduwa sunan nan. Misali kana bukatar ka samu cikakken layin rarraba wutar lantarki, wannan shi ya sa muka shiga aikin abin da ake kira da transmission wannan ne lokacin na farko da aka fara.

A lokacin mun kammala duk bincikenmu muka kaddamar da sayar kayayyaki. Muna gab da sanya hannu a kan takardar kwangila sai ga shi sun bayar da sanarwar kora ta ba tare da ba ni takardar gargadi ko wani abu makamancin haka ba.

Za mu iya cewa wasu tsiraru ne ke hana ruwa gudu don su sake samun wata kwangilar?

Abin da ya faru shi ne kuskuren da muka yi a NIPP, yanzu kuma mun kirkiri abin da ake kira Siemens.

Ina tunanin sun dauke hankalin shugabannin kamfanin rarraba wutar don su kawo Siemens.

Idan ka kalli bidiyon da Kamfanin Siemens suka fitar sun nuna za su samar wa Najeriya wutar lanatarki, sun yi shi ne a Masar.

Duk da cewa matsalar Masar daban da ta Najeriya. Matsalar da Siemens suka warware a Masar matsala ce ta gaba daya idan kana so ka kara abin, to sai ka kara yawan jiragen ruwa, akwai jiragen ruwan da suke da janareta za a iya ajiye su a ruwan Legas.

Kamar abin da ya faru a Legas a lokacin Tinubu wa ya kawo wadannan manyan janaretoci?

Gaskiya ne! Za ka iya kawo irinsu da yawa domin Ghana tana da su. Za ka iya kawo su ka kara janareta. Abin tambayar shi ne matsalarmu ba wai janareta ba ne, matsalar ita ce yadda za a rarraba wutar.

Mece ce shawarka idan da za ka hadu da ’yan takarar Shugaban Kasa da suke son mulkan kasar nan?

Abu na farko shi ne su tsaya su fahimci harkar wutar lantarki, wannan ya hada da yadda ake samun wutar da kuma yadda ake rarraba ta. Ya kamata su fahimci cewa ita wutar lantarki ba kamar ruwa ba ne ba a ajiye ta.

Idan samun wutarka ya kai megawatt 4000 shi kuma yadda za ka raraba yana kan megawatt 2000, to abin da za ka yi shi ne ka samar da wutar megawatt 2000.

A kowane yanayi ana son da nema da kuma bayarwa su zama bai-daya. Idan ana maganar harkar ta lalace, to a lokacin an samu bambanci da nema da bayarwa ba su zo daya ba, don haka akwai abubuwan da ake bukata.

Ya kamata ka samu abin da ake bukata, akwai abin da ake kira ma’ajiyar saura (spinning reserbe).

A yanayin da ake cikin muna amfani da wutar ce ba tare da samar da ma’ajiyar ba. A duk duniya idan kana so ka samar da tsayayyiyar wutar lantarki dole sai ka samar da ma’ajiyar don magance almubazzaranci.

Wajibi ne ka samar da cikakkiyar sa ido da kula. Ya kamata kuma zangonka ya zama ana kula da shi. Abin nufi shi ne dole duk janaretocin su zama suna kan tushen wutar.

Ya kamata kuma su samu mutanen da ba masu cin hanci da almundahana ba ne. Shugaban Kasa shi ne direba abin nufi ya zama mutumin da zai tsaya tsayin daka wajen ganin wutar lantarki ta samu, idan kuma ba haka ba to babu ci gaban da za mu samu.