✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin ‘gobara’ a ginin Ma’aikatar Kudi ta Tarayya

Ma'aikatar kudin ta musanta labarin tashin gobarar.

Zazzafar muhawara ta barke a tsakanin ‘yan Najeriya game da dalilin tashin wuta a wani sashe na  Ma’aikatar Kudi ta Tarayya da ke Abuja.

Wasu ‘yan Najeriya dai sun hau shafukansu na sadarwa suna zargin cewa da gangan aka tashi gobarar don cimma wata muguwar manufa.

Sai dai Ma’aikatar ta Kudi ta fitar da wata sanarwa a shafinta na Twitter tana musanta tashin gobara a ginin.

Batiran da suka kone a Ma'aikatar Kudi ta Tarayya
Batiran da Ma’aikatar Kudi ta Tarayya ta ce sun kama wuta (Hoto: Twitter/@FinMinNigeria

A maimakon haka, inji sanarwar, wasu batira ne da ke ajiye a wani dakin karkashin kasa suka kama wuta, kuma “nan take ma;aikatan tsaron da ke aiki a lokacin suka kashe wutar”.

Lamarin dai ya faru ne da sanyin safiyar Laraba, kuma ba da bata lokaci ba kafofoin sadarwa na zamani suka dauka, har ma wasu ‘yan Najeriya ke cewa watakila an cinna wutar ne da gangan, don boye wata almundahana.