✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin hauhawar farashin Shinkafa — Ministar Kudi

Akwai ’yan Najeriya marasa kishin kasa da ke shigowa da shinkafa mara inganci.

Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-Tsare, Zainab Shamsuna Ahmed, ta bayyana cewa fasa-kwauri ne ke haddasa tashin farashin shinkafa a Najeriya.

Muryar Amurka ya ruwaito Ministar tana bayyana hakan a cikin shirin Siyasa A Yau wanda gidan talabijan na Channels ya saba watsawa.

A cewarta, ayyukan fasa-kwauri na yin mumunan tasiri kan kasuwanci da kuma cutar da ’yan kasar lamarin da ta danganta da abin takaici sakamakon yadda wasu gurbatattun mutane ke shigowa da kayayyaki da gwamnati ta haramta cikin kasa.

Haka kuma, Ministar Kudin ta ce akwai ’yan Najeriya marasa kishin kasa da ke shigowa da shinkafa mara inganci, wasu ma ba za su ciyu ba kuma don neman kazamar riba miyagun ke kawo su cikin gida a zuba a kasuwa.

Zainab ta kuma nanata kokarin Gwamnatin Tarayya na yaki da ayyukan fasa-kwauri, inda ta bayyana cewa hukumar hana fasa kwauri ta kasa, ’yan sanda, jami’an tsaro na farin kaya (DSS) da sauransu na hada gwiwar domin kawar da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa.

Dangane da bukatar sabbin rancen da Majalisun Tarayyar Kasar suka amince Gwamnatin Tarayya ta karbo na baya-bayan nan, Zainab ta ce gwamnati ta kirkiro da tsarin kula da basussuka na matsakaicin lokaci, inda ta ce ba ta hanyar neman umarni daga kotu ne gwamnati ke karbar bashin ba.

Lamarin da ta ce tun farkon shekarar 2021 da mu ke ciki ne gwamnatin tarayya ta shigar da bukatar neman rancen da Majalisun Kasar suka amince da shi ba sabon bukata ba ce.

Ana iya tuna cewa, a watan Mayun ne Shugaba Muhammadu Buhari ya mika bukatar karbo rance ga majalisar dattawar kasar sannan suka amince a karbo a baya-bayan nan.

Shirin neman rance ko lamuni daga kasashen waje na shekarar 2018 zuwa 2020 ya kunshi bukatun neman amincewar majalisa da kudin a jimlace suka kai dala biliyan 36 da miliyan 800, Yuro miliyan 910, da bangaren tallafi na dala miliyan 10.

Tun daga shekarar 2018 zuwa yau ne ‘yan majalisar suka fara amincewa da bukatun neman rance inda suka amince da karbo dala biliyan 8 da miliyan 300 da kuma Yuro miliyan 490 a watan Yuli, daga baya suka kuma amince da gwamnati ta karbo dala biliyan 6 da miliyan 100 a cikin wannan watan da mu ke ciki.