✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin samun takarar Shugaban Kasa ya sa Emefiele sauya wa Naira fasali —Ganduje

Suna son ko dai kar zaben nan ya gudana, ko kuma wata jam’iyyar ta lashe shi.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya zargi Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele da kawo tsarin sauya fasalin takardun naira saboda rashin cimma muradinsa na samun takarar Shugaban Kasa.

An dai yi ta alakanta Gwamnan na CBN da neman takarar Shugaban Kasa a karkashin inuwar jam’iyyar APC, lamarin da ya musanta bayan da wata kungiya ta biya farashin naira miliyan dari wajen saya masa takardun neman izinin shiga takara a jam’iyyar.

Da yake zantawa da BBC Hausa bayan ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Juma’a, Ganduje ya yi zargin Gwamnan CBN din ba ya son ganin Zaben 2023 ya wakana.

An dai shafe sa’o’i ana ganawa tsakanin Shugaban Kasa da gwamnonin APC, inda Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya yi zargin cewa akwai a Fadar Gwamnatin Najeriya da ke yi wa dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu zagon kasa don ya fadi zaben da ke tafe.

El-Rufai ya ce a matsayinsu na gwamnonin Arewa za su yi iyakar kokari wajen ganin mulkin Najeriya, ya koma hannun mutanen Kudu a zabe mai zuwa.

Ya ce “Duk wani zagon kasan da ake in sha Allahu zaben nan mun riga mun ci shi, kuma ba ja da baya za mu yi wannan yaki, za mu kuma kunyatasu mu nuna musu cewa mu ‘yan Arewa ba mutanen banza bane.”

El-Rufai ya kalubalanci masu fakewa a bayan sabon tsarin canjin kudin Najeriya da manufar gurgunta dan takararsu na Shugaban Kasa a jam’iyyar APC.

Ya ce, “yawanci masu yin wannan abu ba ‘yan jam’iyya ba ne, mu muka yi jam’iyyar nan, mu muka yi yakin zabe, su kuma suka kwace gwamnati suke amfani da ita suna jin dadinta, sannan kuma suke yi wa jam’iyya zagon kasa suna yaudarar Shugaban Kasa.”

A nasa bangaren, Ganduje ya ce sun shaida wa Shugaba Buhari cewa sauya fasalin takardun kudin zai jefa ’yan Najeriya cikin halin kaka-nika-yi.

“Wannan ba ajandar APC ba ce, ajanda ce ta wadanda suka zagaye Shugaban Kasa, da kuma shi Gwamnan CBN wanda ya so ya neman ya zama Shugaban Kasa amma abin ya lalace.

“Shi ya sa suke son ko dai kar zaben nan ya gudana, ko kuma wata jam’iyyar ta lashe shi.”

Kan ko gwamnonin za su yi hannu riga da Shugaban Kasa kan wannan manufar, sai Gwamna Ganduje ya ce sam ba wannan magana.

“A’a, mu muna hannun riga da wannan tsari na canjin kudi na Gwamnan Babban Banki da kuma wadanda suka zagaye Shugaban Kasa.”