Daily Trust Aminiya - Dalilin rubuta littafina ga Sarkin Kano – Haruna Birniwa
Subscribe

Haruna Birniwa

Dalilin rubuta littafina ga Sarkin Kano – Haruna Birniwa

Matashin marubuci Haruna Birniwa ya rubuta littafin ‘Wasika Zuwa Ga Sarkin Kano’ cikin wani salo da yake bako a Adabin Hausa. A tattaunawarsa da Aminiya, ya bayyana dalilinsa na zaben wannan salo da abin da littafin ya kunsa:

A takaice wane ne Haruna Birniwa?

Da farko cikakken sunana Haruna Rabi’u Suleiman, haifaffen wani kauye mai suna Birniwa Tasha da ke Karamar Hukumar Birniwa a Jihar Jigawa. An haife ni a 1996, shekara 23 ke nan da suka gabata. Na yi karatun Islamiyya da na boko a Birniwa har zuwa matakin sakandare. Daga nan sai na taho Kano na yi karatun share fagen shiga jami’a a College of Adbanced Studies, Kano. Yanzu haka ina karatun digiri a reshen Jami’ar Bayero da ke garin Gumel. Kuma ina karanta fannin Kimiyyar Sinadarai (B. Sc. (ed) Chemistry), ina aji na uku.

Yaushe ka fara rubuce-rubuce kuma zuwa yanzu littafi nawa ka rubuta,  nawa aka wallafa?

Na fara rubutu tun ina aji shida na firamare, amma a lokacin littafin wadansu nake dauka in kwafe, kamar su Ibada Da Hukunci da Magana Jari Ce. Na fara rubuta nawa na kaina a shekarar 2008, lokacin ina aji biyu na karamar sakandare. Zuwa yanzu na rubuta littattafai guda tara, sai dai har yanzu ban fitar da littafina kasuwa ba.

Ko za ka bayyana sunan uku daga cikin littattafan da bayanin abin da suka kunsa a takaice?

Akwai littafin ‘Burgami A Hannun Beraye’ da ‘Mace Kanwar Shaidan’ da kuma ‘Mu’ijizar Bamaguje.’

Littafin ‘Burgami A Hannun Beraye’ yana dauke ne da labarin wani Sarki da yake son yi wa jama’arsa adalci, sai dai makusantansa, wato fadawa da sauran hakiman masarautar su suke ruguza duk wani shirinsa ba tare da ya sani ba. Shi kuma littafin ‘Mace Kanwar Shaidan,’ wasu tambayoyi ne da labarin yake amsawa, wadanda duk wani dan Adam yana da burin jinsu dangane da tunani da kwakwalwar mahaukata take, yayin da suke cikin hauka. A takaice dai labarin wata mahaukaciya ce da take samun juna biyu a cikin halin da take ciki na hauka. Sai kuma littafin ‘Mu’ujizar Bamaguje’ yana dauke da labari cikin rubutacciyar waka. A Adabin Turawa, ana kiran tsarin da “Nobel in Berse.”

Kana shirin fitar da sabon littafi, yaya sunansa kuma mene ne bayaninsa?

Eh, littafin da nake shirin fitarwa sunansa “Zuwa Ga Sarkin Kano.” Littafin yana dauke da doguwar wasika a bangare na farko sai kuma bangare na biyu da yake dauke da wakoki.

Me ya sa ka rubuta wannan littafi mai sigar wasika ga Sarkin Kano?

Shi wannan littafi yana kunshe ne da sakon mabarata da mashaya kwaya zuwa ga Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II, a kan ya dubi halin da suke ciki na kuncin rayuwa da rashin kyakkyawar makoma. Haka kuma kira ne  da neman wani tallafi na musamman daga wannan fada mai albarka, tallafin da zai ba su damar tsayawa da kafafunsu ba tare da sun je yawon bara ba.

Yaushe wannan littafi zai fito zuwa hannun jama’a?

Insha Allahu ina sa ran fitar da shi a ranar wannan Babbar Sallah.

Ko Sarki da Masarautar Kano sun san da littafin?

Muna kokarin ganawa da shi yanzu haka da muke wannan tattaunawa da kai.

Ko wace gudunmawa kake ganin littafin nan zai ba al’umma idan ya fito?

Littafin zai daidaita tunanin al’umma a kan irin kallon da ake yi wa mabarata da mashaya kwaya na rashin kima a cikin al’umma. Sannan zai bai wa wadanda abin ya shafa sanyin zuciya, domin ko babu komai sun samu damar da duniya za ta fahimci zancen da yake dauke a zukatansu. Bugu da kari, zai ba gwamnati da mahukunta damar gane hanyoyin da za su bi wajen shawo kan matsalar barace-barace da shaye-shaye cikin sauki.

Me ya sa ka zabi Sarkin Kano, ka rubuta masa wannan wasika, duk da cewa Gwamna ne ke mulkin jiha ta fuskar hukuma da sarrafa al’amuran al’umma?

Sarkin Kano shi ne sabon waliyyi da zai kawo canji a rayuwar talakawa. Shi ne yake tsayawa koyaushe a bangarensu a kan hakkinsu, ka ga ke nan tallafa wa talaka ba sabon aiki ba ne a gare shi.

Daga karshe, wane kira ke gare ka ga shugabanni da al’umma dangane da wannan littafi naka?

Su bar duk abin da suke da zarar littafin ya fito kasuwa su karanta, domin akwai komai da suke bukata don tafiyar da rayuwa a cikinsa.

More Stories