✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin rufe masallacin Sheikh Abduljabbar —Ganduje

Gwamnan ya kalubanci malamin ya kawo hirar kwamishinan da ya ce an zalunce shi.

Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana dalilin da ya sa ya rufe masallacin Sheikh Abduljabbar tare da hana shi gabatar da wa’azai a Jihar.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa ba za ta sa ido wani mutum ya rika tunzura mutane su ta da rikici a jihar ba, yana mai musanta zargin malamin cewar siyasa ce ta sa gwamnan ya dauki matakin da ya kunshi hana sanya karatun malamin a kafafen yada labarai.

Da yake tatraunawa da Sashen Hausa na BBC, Ganduje ya ce “Muna lura da abubuwan da yake aikatawa kuma hukumomin tsaro na bin lamarin a sannu, kamar yadda kuke gani mun dauki mataki.

“Mun dauki mataki kan abin da yake yi ne saboda gudun tayar da fitina a Kano. Jami’an tsaro sun yi aikinsu na tabbatar da tsaro kuma ina fatan jama’a za su fahimci hakan,” a cewar Gwamna Ganduje.

Da aka tambayi gwamnan me ya sa gwamnatin jihar ta yi watsi da bukatar Sheikh Abduljabbar na yin mukabala da malaman da ke zarginsa da tunzura jama’a da batancin da Sahabban Manzon Allah (SAW), sai gwamnan ya kada baki ya ce: “Gwamnati ba ta yi watsi da shi ba, bari na fada muku mayaudari ne, lokacin da yake cin mutuncin Sahabbai, gwamnati ce ta ba shi damar yin hakan?

“Dalilin da ya sa gwamnati ta dauki mataki shi ne saboda ya ce duk wanda ya je kusa da masallacinsa a yanka shi.”

Karya Sheikh Abduljabbar yake yi

Gwamna Ganduje ya ce hukuncin da gwamnatinsa ta dauka ba shi da alaka da siyasa, amma idan malamin na ganin ba haka ba ne, to ya fito fagen siyasa su kara.

“Karya yake yi, babu wata alaka tsakanin wannan hukuncin da siyasa; Na ji har cewa yake wa magoya bayansa su sabunta rajistar katin zabe, idan yana ganin ya isa ya shigo siyasa mu kara ya ga abin da zai faru.

“Saboda yana ganin wasu ’yan tsirarun mutane ya masa tafi shi ne yake cewa su sabunta rajistarsu, za mu ga abin da zai faru, Allah na tare da masu gaskiya a ko yaushe.”

Ganduje ya kalubanci Sheikh Abduljabbar

A martanins kan kalaman Sheikh Abduljabbar na cewa Kwamishinan Ilimi ya bayyana a gidan rediyo cewa an zalunce shi, gwamnan ya kakubalanci malamin ya kawo faifan jawabin Kwamishinan.

“Muna so ya fito ya fadi inda Kwamishina ya fadi hakan, mu kuma muna da bidiyon inda ya ke cewa duk wanda yaje masallacinsa a yanka shi. Wannan furuci rikici zai haifar, kuma gwamnati ba za ta amince ba,” inji Ganduje.

Zaben Gwamnan Kano a 2019

Malamin wanda ya yi fice wajen sukar wasu daga cikin Sahabban Manzon Allah (SAW), ya ce hukuncin da gwamnan ya dauka a kansa na da nasaba da rashin goyon bayansa da ya yi a zaben 2019.

Zaben Gwamnan Kano da aka gudanar tsakanin Ganduje na jam’iyyar APC da Abba Kabir Yusif na PDP, ya bar baya da kura tun a wancan lokaci.

Raddin Sheikh Abduljabbar ga Ganduje

A zantawarsa da manema labarai ranar Alhamis bayna umarnin Gwamnain Jihar Kano, Sheikh Abduljabbar ya ce, “Dalilin yin hakan a bayyana nake, shi wanda ya ba da umarnin da ma ya sha fadar cewa ba ya yafiya.

“Ban goyi bayansa lokacin zabe ba, kuma ya yi alkawarin ramawa; har yana cewa tsiyar nasara sai za shi gida. To sai dai bai iya tsiyar ba, saboda wannan siyasa ce kawai.

“Na sanar da magoya bayana da su sabunta rajistar zabensu kafin zabe mai zuwa. Na gode Allah saboda rigima ta da malamai na ke yi, amma sai ga shi gwamnati ta ara ta yafa.

“Wannan ya nuna malaman ba su amsar tambayoyina. Ita gwamnatin ta ya aka yi tasan ina neman tada fitina? Sun duba litattafan da nake kafa hujja da su kafin yanke hukunci? Shin suna ma da ilimin abin da ake magana a kai?

“Ya kamata a ce sun duba litattafan da nake kafa hujja da su, amma sai suka min rashin adalci,” cewar Sheikh Abduljabbar.