✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin rufe masana’antun Kano da Kaduna —Aminu Dantata

Damuwar Alhaji Aminu Dantata kan yadda aka rufe masana’antu a jihohin Kano da Kaduna

Alhaji Aminu Dantata na daya daga cikin tsofaffin masu arzikin da ake maganarsu, har yau a Najeriya.

A wata hira ta musamman da Aminya ta yi da shi, Alhaji Aminu Dantata ya nuna takaicinsa kan yadda aka rufe masana’antu da dama a jihohin Kano da Kaduna, wanda hakan ya yi sanadin rasa aikin dubban matasa.

Attajirin wanda ya fara neman kudi ne tun yana matashi ya ce babban dalilin da ya kawo rufe wadannan masana’antu, shi ne rashin kula da mayar da hankali daga masu masana’antun.

Alhaji Aminu Dantata ya tabbatar da cewa yana da hannayen jari a kusan dukkan masana’antun da suke aiki a kasar nan.

Ya ce yana da hannayen jari, a dukkan kamfanonin da suke aiki a Kano da Kaduna sama da shekara 20.

A yayin da masu kudi da shekaru irin nasa ke tunanin su je su huta, shi kuwa shirye-shirye yake yi na sake bude Masakar Fine Ted Textile da ke Kaduna, wadda yake da kashi 87, na hannun jarin masakar.

Har ila yau a matsayin Alhaji Aminu Dantata na mai shekara 89 a duniya, a yanzu ya shirya sanya jari a harkokin noma, inda ya shirya noma babbar gonarsa da ke garin Kura a Jihar Kano, mai fadin eka 5,000.

Ya ce ya shirya zai noma shinkafa da masara don bunkasa samar da abinci a kasa da samar da ayyukan yi, ga al’umma.