✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin zaftare wa Juventus maki 15 a Serie A

Juventus din na fuskantar wani binciken kuma daga UEFA.

An zaftare wa Juventus maki 15 sakamakon wani bincike da aka yi a kan cinikayyarta ta musayar ‘yan wasa ta baya, kamar yadda Hukumar Kwallon Kafa ta Italiya ta bayyana.

An zargi kungiyar ta babbar gasar kwallon kafa ta Italiya, Serie A, da laifin lissafin dokin-rano, inda ta yi karyar yawan ribar da ta samu daga cinikin ‘yan wasa a takardun bayanan kudadenta.

Kungiyar tana matsayi na uku ne a tebur, to amma da wannan hukuncin yanzu ta zama ta goma.

A watan Nuwamba darektocin kungiyar ciki har da tsohon shugabanta Andrea Agnelli da mataimakinsa Pavel Nedved, suka ajiye aiki.

A martanin da ta mayar kan hukuncin ta ce ba wani abu da ya saba doka da ta aikata, kuma ta ce za ta daukaka kara a kai.

Masu gabatar da kara sun bukaci a yanke wa kungiyar maki tara ne amma kuma ita hukumar kwallon kafar ta Italiya, sai ta tsananta hukuncin.

Tsohon darektan wasanni na kungiyar Fabio Paratici, wanda yanzu shi ne manajan darektan Tottenham, an haramta masa shiga harkokin wasa tsawon wata 30.

Jumullar shugabannin kungiyar 11 na da da na yanzu ne aka yi wa hukunci danban-daban sakamakon binciken.

Juventus din na fuskantar wani binciken kuma daga Hukumar Kwallon Kafa ta Turai, UEFA kan batun laisisinta da kuma saba ka’idojin cinikin ‘yan wasa, wanda aka sanar a watan da ya gabata.

Wasa na gaba da Juventus din za ta yi a gidanta ne da Atalanta a ranar Lahadi.