✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilinmu na Sallar Idi ran Laraba —Dahiru Bauchi

Shehin malamin ya ce an tabbar musu da ganin wata ranar Talata a sassan Najeriya.

Babban Shehin Darikar, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya ce ya jagoranci hawan Idin Karamar Sallah a ranar Laraba ne bayan samun tabbacin ganin jinjirin watan Shawwal a ranar Talata.

Shehin malamin ya yi bayanin ne bayan saukowa daga sallar idin da aka gudanar a gidansa da ke Bauchi a safiyar Talata.

“Dangane da wannan labarai na cewa wata ya tabbatar, abin da aka ce adalai guda biyu idan sun gani ya isar ma jama’a, ko kuma jama’a masu yawa idan sun ga watan,” inji shi.

Sai dai kuma Idin da shehin da dubban mabiyansa suka gudanar ta saba umarnin Sarkin Musulumi na cewa ranar Alhamis za a yi Karamar Sallah bayan an sha ruwan azumi na 30 a ranar Laraba, saboda ba a ga wata a ranar Talatar ba.

Amma ya yi bayani cewa “An ga wata [ranar Talata] a wurare irin su Gombe da Gadau da kuma Kebbi,” kuma mutanen da suka ga watan “saboda suna da yawa,”  kuma ba shi da ikon karyata mutanen da suka tabbatar da ganin watan.

“Shi ya sa yanzu muka zo muka gudanar da sallar Idi domin watan Ramadana ya kare, watan Shawwal ya shigo,” inji shi

Ya yi jawabin ne bayan saukowa daga sallar idin da dansa, Tijjani Dahiru Bauchi ya yi limanci, shi shehin malamin ya kasance a cikin mamu.