✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dambarwar APC: Abin da Gwamnan Neja ya yi daidai ne —Buni

Buni ya tabbatar da duk abin da Gwamnan Neja ya yi a shugabancin jam'iyyar APC

Shugaban Kwamitin Riko da Shirya Babban Taron Jam’iyyar APC na Kasa kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya tabbatar da duk hukuncin da Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya yanke a jam’iyyar.

Buni ya sanar da haka ne ta wata sanarwa da shi da kansa ya sanya wa hannu a ranar Alhamis, yana tabbatar da jerin sunayen da Bello ya fitar na mambobin kananan kwamitcomin taron da za a yi ranar 26 ga watan Maris da muke ciki.

Sanarwar ta ce, “Idan ba a manta ba na mika ragamar shugabanci ga Mai Girma Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello a hukumance domin in samu zuwa duba lafiyata.

“Saboda haka duk matakan da aka dauka a karkashin jagorancin Mukaddashin Shugaban Jam’iyya za su ci gaba da aiki.

“Jam’iyya na kira ga mambobinta da magoya bayanta da su bayar da hadin yadda ya kamata domin gudanar da babban taronmu da zai gudana a ranar 26 ga watan Maris, 2022 cikin nasara.”

Hakan na zuwa ne bayan wani sabon jerin sunayen mambobin kwamitocin da Sakataren Jam’iyyar na Kasa, Sanata James Akpanudeodehe ya fitar, wadda ta saba da jerin sunayen da Bello ya sanya wa hannu ya kuma fitar da farko.

APC ta kori Sakatarenta na Kasa

Wannan sanarwa ta Buni tamkar tabbatarwa ce ga matakin da Kwamitin Rikon Jam’iyyar ya dauka na sallamar Sakataren Jam’iyyar na Kasa, Sanata James Akpanudeodehe, daga mukaminsa.

Bayanin sallamar ya fito ne a ranar Alhamis, washegarin da Sanata James Akpanudoedehe ya ci gaba da aiki, ya kuma jagoranci fara sayar da takardun neman tsayawa takarar kujerun shugabancin jam’iyyar.

A matsayinsa na Sakataren Jam’iyya, Sanata James Akpanudoedehe, shi ne mutumin da ke jagorantar kwamitin gudanarwar APC a duk lokacin da Shugaban Riko da Kwamitin Babban Taron Jam’iyyar, wato Gwmanan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ba ya nan.

Amma Gwamna Abubakar Sani Bello, wanda a baya ya yi ikirarin zama Mukaddashin Shugaban Rikon Jam’iyyar, da sauran mambobin kwamitin babban taron mai mutum 10 wadanda ke gudanar da jam’iyyar tun daga watan Yunin 2020, sun sanar cewa sun yanke kauna daga irin kamun ludayin Sanata Akpanudoedehe a jam’iyyar.

Sanata Akpanudeohehe ya fara shiga tsaka-mai-wuya ne a makon jiya bayan  rana tsaka Bello da wasu mukarrabansa sun yi ikirarin karbe ragamar shugabancin jam’iyyar, har suka gudanar ta taron gaggawa kan shirye-shiryen babban taron, a yayin da Shugaban Rikon Jam’iyyar, Mai Mala Buni, ke kasar waje.

Sanarwar da suka fitar na dauke da sa hannun Gwamna Bello da sauran mambobin kwamitin — Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ken Nnamani; Sanata Yususf Abubakar Yususf, Farfesa Tahir Mamman, David Lyon, Akinremi Olaide, Barista Ismaeel Ahmed, Dokta James Lalu, da kuma Stella Okotete.

Duk mambobin kwamitin rikon sun riga sun rattaba hannu kan takardar, in banda in banda Mai Mala Buni, wande ka kasar waje.

Kawo yanzu dai ba a kai ga jin ta bakin Sanat Akpanudoedehe ba.