✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dambatta, NCC da kokarin zakulo Zuckerbergs din Najeriya

A littafinsa mai suna Darasi 21 na Karni na 21, fitaccen marubuci Yubal Noah Harari ya rika fadakar da mu kan kalubalen da juyin juya-halin…

A littafinsa mai suna Darasi 21 na Karni na 21, fitaccen marubuci Yubal Noah Harari ya rika fadakar da mu kan kalubalen da juyin juya-halin masana’antu na karni na hudu ke haifarwa.

“Babu shakka juyin juya-halin kimiyya zai yi karfi nan gaba kadan kuma zai kalubalanci dan Adam fiye da yadda muke tsammani. Duk wani lamari da ke da alaka da dan Adam zai gamu da kalubale wajen fuskantar juyin juya-hali biyu na kimiyyar sadarwa da ta kere-kere,” inji shi.

Harari ya bayyana cewa akwai yiwuwar ba wai kawai kararrawar da ke bugawa a kunnuwanmu da karfi ba har ma da yadda barazanar da juyin juya-halin masana’antun ke yi mana gizo a fuska.

Saboda haka ya zama wajibi kan dukkan wadanda za su kasance jagorori na wannan juyin juya-halin da ita kanta daukacin duniyar ta shirya, ba wai kawai wajen tattara masu hikima ba, har ma da sanya kudade wajen cimma burin da ake so.

Hakika ba za a guje wa kasancewar jirgin zai tashi ba tare da wadanda suka kasa shiga cikinsa ba, kuma gaskiyar ita ce hakan zai zamo wani babban bala’i.

Misali batun kasancewar kimiyya da kere-kere sun game duniya ya riga ya sauya batun tattalin arzikin duniya. Dabarun da a da ake daukarsu shafa labari shuni yanzu sun zama jigon tattalin arzikinmu. A karon farko a tarihinmu kunshin data na maye gurbin albarkatun mai a matsayinsa na muhimmin abin dogaron tattalin arzikin duniya. Matasa masu fasaha na maye gurbin tsofaffin masana a fannnin mai a jerin sunayen mafiya dukiya a duniya na Mujallar Forbes, kuma hakan zai ci gaba da kasancewa shekaru da dama nan gaba.

Abin mamakin ma shi ne yadda kamfanonin da ke tasowa suka kai makura a shekarar 2017. A rabin lokaci kadai kamar yadda mujallar GSMA ta wallafa jarin kamfanoni masu zaman kansu da kamfanoni masu zuba jari da hukumomi tuni suka zuba jarin Dala tiriliyan daya da biliyan biyu a wannan bangare.

Idan sauran kasashen duniya za su fuskanci batun kirkira tare da sanya jarin kudi wajen daukar nauyin masu bincike matasa, kan binciken yadda za a magance matsaloli, duk da cewa akwai alaka a tsakanin bincike da ingattaciyar rayuwa, a Najeriya ba za mu rika zuwa wani wuri ba don neman maganin matsalolinmu.

Za mu iya cewa a nan ne Farfesa Garba Dambatta, Babban Shugaban Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ya yi fice inda ya cancanci mu yaba masa.

Saboda zai iya yin alfaharin cimma nasorori masu yawa kamar cimma burin da ake ganin kamar ba zai yiwu ba na adadin da aka sanya kan samar da Intanet, irin yadda Dambatta yake tallafa wa bincike da kirkira ya wuce duk yadda ake zato.

Kamar a sauran bangarorin da aka ga muhimmancin jagorancinsa, Dambatta ya zo Hukumar NCC ya samu yanayi inda ake tafiyar da batun bincike da bunkasawa a matsayin karamin sashe amma sai ya bunkasa shi zuwa babban sashe a hukumar.

Bisa la’akari da biyu daga cikin ajandojinsa takwas, bunkasa kirkirar kimiyya da kere-kere da samar da damar zuba jari da bunkasa hadin gwiwa, Dambatta ya bude kofa sosai inda ya fadada hadin gwiwa da masana don cimma alfanun binciken.

“Ka san masana’antar tarho aba ce ta musamman. Sababbin fasahohi kullum bullowa suke yi tare da sababbin kalubale. Kuma ta hanyar bincike da bunkasawa za mu iya magance kalubale a masana’antar tare da bunkasa ayyukan da kamfanonin masana’antar suke yi wa ’yan Najeriya. Za mu iya haka ta hanyar yin amfani da darussan da muka samu, tarin ilimin da ke jibge a jami’o’in Najeriya. Kuma za mu iya ganin tarin takardun bincike daga jami’o’in Najeriya kuma muna sa ran wadannan bukatu  za su samar da wata turba da za mu iya cin moriyarsu nan gaba kadan ta yadda za mu farfado da bangaren masana’antu na tattalin arziki,’’ inji Farfesan Kimiyyar Sadarwar, yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a wani biki da aka shirya don bayar da matsayin Farfesa a wasu jami’o’in kasar nan biyu kwanakin baya.

Amma har yanzu wadansunmu za su iya tambaya: “Me ya sa mai sanya ido ce kawai ke tafiyar da komai da kanta maimakon masana’antar da kanta?”

Mista Ephraim Nwokonneya, Daraktan Bincike da Bunkasa Harkoki na Hukumar ya bayar da gamsashshiyar amsa.

“Mun shigo ciki ne saboda ba kamar a kasashen da suka ci gaba ba inda masana’antar ke bunkasawa tare da tallafa wa bincike a nan abin ba haka yake ba.’’

Nwokonneya, wanda ya yaba wa Shugabar Hukumar NCC din saboda kokarin da ya yi na bunkasa bincike ya ce Farfesa Dambatta mutum ne wanda yake aiki da cikawa  ta hanyar sanya bincike da bunkasawa a kan gaba na hukumar.

“Farfesa Dambatta ya fahimci cewa masana’antar abubuwa sun yi mata yawa kamar bangaren ayyukan murya da wasu abubuwan ci gaba na bangaren Intanet da ayyukan data da wasu ayyuka na musamman da wasu damarmaki da za a iya cimma burinsu ta hanyar yin amfani da bincike da bunkasawa,” inji shi.

A yanzu ayyukan bincike 26 da hukumar ke daukar nauyi a wasu jami’o’in kasar nan na ci gaba inda aka kusa kammala biyu daga ciki.

Hakan ya hada da: Kera na’urar mutum-mutumi mai tafiya ta sadarwar tarho da kera na’urar sadarwa don amfanin gida da bunkasawa tare da samar da na’urar tattara data da mai sanya ido kan sadarwar manyan kamfanoni da sauransu.

Dukkan wadannan abubuwa sun samu ne saboda namijin kokarin da Dambatta yake yi wajen bunkasa masana’antar ta hanyar bincike da bunkasa harkoki wajen tunkarar balahirar da Harari ya yi hasashen faruwarta a nan gaba kuma nasarar hakan ta samu ne saboda jagoranci nagari wajen gudanar da harkokin hukumar da ke sanya idon.

Matasan da ke da fasahar kirkira da hukumar ke daukar nauyinsu a duniyar sadarwa a birnin Busan da ke Koriya ta Kudu shekara biyu da suka gabata sun bai wa duniya hasken abin da ake tsammani. Kowa ya zura ido ga masana da ke jami’o’i su bullo da wani salo da zai sanya Najeriya a turbar kirkira ta duniya.

Musa, Mataimaki ne na Musamman Kan Harkokin Watsa Labarai ga Babban Shugaban Hukumar NCC, ya rubuto wannan makala ce daga Abuja.