✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Damfarar masu neman aiki ta kai Daraktan Gwamnatin Sakkwato kurkuku

Kotu ta aike da wani darakta a Gwamnatin Jihar Sakkwato zuwa gidan yari saboda damfarar wasu masu neman aiki Naira milian 1.3

Kotu ta aike da wani darakta a Gwamnatin Jihar Sakkwato zuwa gidan yari saboda damfarar wasu masu neman aiki Naira milian 1.3.

A ranar Laraba, Babbar Kotun Tarayya da ke Sakkawto ta aiki da Darakta Hassan Bello na Hukumar Kayyaki ta jihar zuwa gidan yari, bayan Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) ta gurfanar da shi.

Lauyan EFCC, Hannafi Sa’ad, ya shaida wa kotun cewa, Hassan, wanda shi ne Darakan Gudanarwa a hukumarsa, ya karbi karbi kudade daga wasu mutum uku bisa alkawarin ba su aiki a gaban wani mai suna Dahiru Muhammad a matsayin shaida.

Lauyan ya ce wanda ake zargin ya kuma bai wa Aliyu Adamu-Tsaki, Yusuf Abubakar da Yahaya Salihu takardun daukar aiki na bogi, a watan Agustan 2021.

Daga baya ne aka gano cewa takardun daukar aikin da ya ba su na jabu ne, hasali ma hukumarsa ba ta dauki sabbin ma’aikata ba.

Lauyan mai kare wanda ake zargi, Aminu Mustapha, ya bukaci a bayar da belinsa, amma lauyan EFCC ya kalubalanci hakan, yana mai cewa zai bukaci karin lokaci domin yin nazari kan lamarin.

Daga nan alkalin kotun, Mai Sharia’a Ahmad Mahmud, ya bayar da umarnin tsare wanda ake zargin a gidan yari har zuwa ranar ci gaba da sauraron karar.

Sannan ya dage shari’ar zuwa ranar 4 ga watan Oktoba mai kamawa domin sauraron bukatar belin wanda ake tuhuma.