✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Damisa ta kai hari a cikin kotu

Kafar labarai ta Daily Mirrow ta ruwaito cewa bidiyon harin damisar da aka dauka a kan layi ya nuna yadda jama'a suka dauki wani mutum…

Wata damisa da ta kwace ta kai wa hari a cikin wata kotu inda ta raunata mutane da da dama.

Hukumomin kasar Indiya sun ce damisar ta raunata mutum biyar a zauren kotun da ke wani bene, lamarin da ya haddasa fargaba matuka.

Wani dan sanda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, “Damisar ta rika zagaye harabar kotun, inda ta jikkata akalla mutum biyar,”

Da kyar, daga baya ’yan sanda da jami’an kotu suka shawo kan dabbar, domin takaita barnar da ta yi, a Babbar Kotun Majistaren da ke Ghaziabad a yankin Uttar Pradesh na kasar Indiya.

Mutane da dama ne dai suka samu rauni bayan harin damisar, kuma an garzaya da su kotu domin samun kulawa.

Harin damisa
Hoton wani da ya ji rauni a harin da damisar. (Hoto: Daily Mirrow/Twitter

Kafar labarai ta Daily Mirrow ta ruwaito cewa bidiyon harin damisar da aka dauka a kan layi ya nuna yadda jama’a suka dauki wani mutum da ya samu, za su kai shi asibiti.

Duni dai jami’an tsaro suka killace dabbar a keji.