✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan APC na so a hana Tinubu shiga takara saboda zargin yin karya a takardun karatunsa

Ya ce zarge-zarge kan Tinubun na iya yin illa ga APC yayin zabe

Wani dan jam’iyyar APC daga Jihar Kano ya roki Kwamitin Tantance masu neman takarar Shugaban Kasa ya hana Bola Tinubu shiga zaben fid da gwanin jam’iyyar saboda zargin karya a takardun karatunsa da kuma shekaru.

Mutumin, mai suna Sagir Mai Iyali dai yana zargin tsohon Gwamnan na Jihar Legas ne da yin karyar kammala karatu a Jami’ar Chicago da ke Amurka.

A cikin wata takardar korafi mai dauke da kwanan watan 17 ga watan Mayun 2022 wacce aka aike wa Shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu da Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC), Farfesa Mahmud Yakubu, mutumin ya yi zargin cewa Tinubu ya yi karya a takardun da ya gabatar wa INEC a 1999 lokacin da zai tsaya takarar Gwamnan Legas.

Kwamitin Tantance ’Yan Takarar dai na karkashin tsohon Shugaban jam’iyyar, John Oyegun ne, kuma ya fara zamansa ne a otal din Transcorp Hilton da ke Abuja, gabanin zaben fid da gwanin jam’iyyar da za a yi ranakun shida da bakwai ga watan Yuni.

Mai Iyali ya kuma yi zargin cewa akwai kumbiya-kumbiya a ainihin shekarun Tinubun, wanda ya zarga da boye-boye, inda ya ce hakan na iya shafar makomar takarar APC.

Wani bangare daga wasikar ya ce, “Tinubu ya yi ikirarin kammala karatu a Jami’ar Chicago, amma ta bayyana hakan ba gaskiya ba ne.

“Ba wai kawai ya gabatar wa INEC takardar ba ne a ranar 20 ga watan Disamban 1999, ya kuma samo takardar Babbar Kotun Ikeja da ke Legas da ke nuna cewa takardar karatunsa ta bata, a ranar 29 ga watan Disamban 1998,” inji wasikar.

Sai dai a baya, Tinubu ya amsa cewa akwai kura-kurai a cikin fom din takarar da ya mika wa INEC a 1999.

Amma daga bisani Majalisar Dokokin Jihar Legas ta wanke shi kan zargin karyar takardun, ko da yake an zargi ’yan majalisar da yin gaggawa a yayin binciken nasu.