✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan bindiga ya harbe tsohuwar matarsa da wasu mutum 5

Mutum shida suka mutu sakamakon harin

Wani dan bindiga ya harbe mutum shida, ciki har da tsohuwar matarsa a yankin Arkabutla da ke Arewacin Jihar Mississippi a Amurka.

Harin, wanda ya auku da safiyar Juma’a, ya yi sanadiyyar mutuwar mutanen, ciki har da tsohuwar matar maharin.

Haka nan, harin ya rutsa da mijin mahaifiyar maharin da kuma wata ’yar uwarsa, in ji ’yan sandan yankin.

Bayanan ’yan sanda sun nuna maharin ya kashe mutanen ne a wurare daban-daban.

Gwamnan Mississippi, Tate Reeves, ya ce ya samu rahoto kan hare-haren da aka kai a yankin a baya-bayan nan.

Matsalar yawan harbe mutane da bindiga dai ta zama ruwan dare a Amurka a ’yan shekarun nan, inda ’yan bindiga kan aika mutane lahira, ciki har da wadanda ba su ji ba, ba su gani ba.