✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan dambe ya mutu bayan an yi masa mahangurba

Dan damben ya fadi kasa warwas bayan da ya sha wawan naushi a habarsa.

Wani dan dambe ya gamu da ajalinsa a ba tsakiyar filin wasa, bayan da abokin karawarsa ya yi masa wawan naushi.

An naushi Chukwuemeka Igboanugo ne a habarsa a yayin da suke tsaka da karawa, inda ya fadi kasa warwas, ya kasa tashi wanda hakan ya sa alkalin wasan, ya ayyana abokin karawar tasa dan asalin Jihar Anambra a matsayin wanda ya yi nasara.

Daga bisani hankali ya tashi ganin cewa Chukwuemeka ya kasa tashi, inda masu ba da agajin gaggawa suka garzaya da shi zuwa asibiti, amma likitoci suka ce rai ya riga ya yi halinsa.

Kakakin ’yan sandan Jihar Delta, Bright Edafe ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba.

Hukumar Shirya Wasanni ta Kasa ce ta shirya gasar a karo na 21 a Asaba a Jihar Delta, inda dan wasan mai ya rasa ransa, yayin karawa da abokin dambensa.

Yanzu haka dai, Kungiyar ’Yan Wasan Damben Najeriya da kuma Gwamnatin Jihar Delta ba su ce komai ba dangane da mutuwar dan damben.