✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan hakin da ka raina

Canjin sheka ga dan siyasar Najeriya ba wani abin damuwa ba ne domin a ganinsa ba kansa ne farau ba, wasu da yawa ma sun…

Canjin sheka ga dan siyasar Najeriya ba wani abin damuwa ba ne domin a ganinsa ba kansa ne farau ba, wasu da yawa ma sun yi a gabansa.  A jamhuriya ta farko an sha yin haka hatta a cikin majalisa; a jamhuriya ta biyu kuwa an hana yin haka a zahiri da badini;  sa’annan kuma a wannan marrar cikin ruwan sanyi ake canja jam’iyya, kuma ana iya haka a majalisa idan akwai rarrabuwar kawunan ‘ya’yan wata jam’iyya.  To me ke sa ana yin haka? Mene ne kuwa, ban da kawazucin  neman mukami ta hanyar tsayawa takara?  Wannan ne ke kai manyan ‘yan siyasa tsilla-tsilla daga wannan jam’iyyar zuwa waccan don su yi takarar shugabancin kasa.  

Shugaba Muhammadu Buhari ya taba barin jam’iyyar ANPP sa’ilin da takun sakar da suke  da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sardauna  Ibrahim Shekarau ta tsananta, a jam’iyyarsu ta ANPP,  ya kuma kafa wata sabuwa ta CPC don ya yi takarar shugabancin kasa a 2011. Haka nan ma Wazirin Adamawa, Alhaji Atiku Abubakar ya sha zarya tsakankanin wasu jam’iyyun da suka hada da ta PDP da ta AC da kuma APC don ya tsaya takarar zaben da za ta kai shi ga biyan bukatarsa ta shugabancin kasar nan kafin komawarsa ga Mahaliccinsa. 

To, ba ga jiga-jigan ‘yan siyasa masu neman mukamin shugaban kasa canjin sheka ta tsaya ba, akwai wasu ‘yan ku-ci-ku-ba-ni  ma da ke yawan yin  haka.  Alhaji Isa Yuguda ya ci zaben Gwamnan Jihar Bauchi a karo na biyu karkashin jam’iyyar ANPP, amma bayan  wani dan gajeren  lokaci da rantsar da shi sai ya fice daga jam’iyyar da aka zabe shi a karkashinta, ya yi ridda zuwa wacce ta yi adawa da shi kafin zaben. A yanzu haka akwai wasu gwamnonin da ke bisa mulki a wasu jihohin Arewa,  wadanda  asalinsu PDP ne, kamar yadda ake da ‘yan majalisun dattijai da ta tarayya, ‘ya’yan jam’iyyar APC ne  wadanda suka taba yin  PDP. 

To, ashe sanarwar da Waziri Atiku Abubakar ya bayar ranar Juma’ar da ta gabata cewa ya fice daga  jam’iyyar APC, yana kuma shirin komawa wata wacce bai fayyace ba, al’amari ne da bai zo ma kowa a ba-zata ba. Yana da ‘yancin yin haka, domin  shan koko daukar rai ne. To, amma tun da haka ne ai ba wani mai damuwa a cikin jam’iyyar APC idan  Atiku ya fice daga ciki, balle har ya yi masa bi-ta-kulli, ko kuma a yi ta gasa mar maganganu masu nuna cewa akwai wata kullaliya, ko kuma ya bar baya da kura.  A cewar Waziri Atiku shi ba zai iya kasancewa cikin jam’iyyar  da ba ta jin shawara ba, wacce ke yin gaban kanta bisa dukkan al’umurran da suka shafi ‘ya’yanta , sa’annan kuma ba ruwanta da bin ka’idojin da ke kunshe cikin kundin tsarin gudanar da harkokinta.

Idan kuwa haka ne yana da kwakkwarar hujja,  irin ta wasu ‘ya’yan jam’iyyar a wasu wurare da ke ta yawan guna-guni game da yadda aka maishe su ‘ya’yan bora wadanda ba a yi da su, sun kuma rigaya sun fahimci cewa ba za a taba ba su damar yin rawar gaban hantsi ba nan gaba a dukkan wasu aikace-aikacen da suka shafi jam’iyyar. Su ma  lokaci kawai suke jira su kama gabansu, domin a cewarsu gadon Ari sai Farna, ramin kura kuma sai ‘ya’yanta. 

To amma Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir el-Rufa’i ya gaggauta sukan lamirin ficewar  da Waziri Atiku  ya yi daga jam’iyyarsu wacce wasu ‘ya’yanta da yawa suka wanke wa hannu a-ka, suka kuma dawo daga rakiyarta domin rashin ciccika alkawura da kuma rashin tabuka wani abin alheri ga jama’a tun farkon hawanta mulki,  illa janyo matsalolin da suka jejjefa jama’a cikin kangin wahala da talauci.  Gwamna Nasir ya ce jam’iyyar APC na murna da ficewar Waziri Atiku daga cikinta, ya kuma kara da cewa Allah-raka taki gona. To abin tambaya a nan tsakanin  Waziri Atiku da jam’iyyar APC  wane ne ke murna da barin wani?  Atiku ne ko jam’iyyar APC?  Idan har Atiku ya zame taki, ashe duk  manomin da zai nufi gonarsa zai fi kowa murna domin kuwa arziki ne ya zo masa, hakan kuma rashi ne ga jam’iyyar APC. Ai inda duk taki yake nan albarka za ta kasance. To, ba sai kawai a amsa addu’ar Gwamna Nasir da cewa Amin ba?

Gwamna Nasir ya ce  Waziri Atiku ya fice daga jam’iyyar APC ne don ya ga ba zai samu sukunin takarar zama shugaban kasa ba a cikinta, domin kuwa daga cikin gwamnonin jam’iyyar APC ashirin da hudu ba wanda zai bi shi domin  rabinsu na tare da Shugaba Muhammadu Buhari ne, to yana da tabbacin cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai sake tsayawa takara a karo na biyu, kuma wadancan gwamnonin kusan rabi ba za su kauce ba su bi Yarima su sha kida ba? Daga yanzu zuwa lokacin da za a fara yakin neman zabe gadan-gadan, Allah ne kadai Ya san abubuwan da za su iya wakana, ‘ya’yan jam’iyyar APC da yawa na  iya zaizayewa su bi Waziri Atiku, tun da dai ga  shi nan ficewarsa ta sa jam’iyyar APC ta fara famfara. Ai ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare.

Waziri Atiku dai bai ce ga jam’iyyar da zai koma ba tukuna, ko da yake ana kyautata zaton cewa zai yi kome ne a PDP. Idan kuwa haka ne ana iya cewa PDP  ta samu ingantaccen takin da zai amfani gwamnoninta guda goma sha daya da ‘yan  majalisunta na dattijai da wakilai wadanda  yawansu ya kusa yin kunnen doki da na APC mai rinjaye. A jihohi kuma jam’iyyar PDP ba kanwar lasa ce ba, kashin bugun kashi ce, kuma da ma can a nan jihohin Arewa ba ita aka ki ba, Goodluck Jonathan ne ya janyo mata bakin jini saboda kulafucinsa na dawwama bisa mulki. Ashe ke nan idan ba an yi da gaske ne ba tana iya farfadowa ta kuma ba jam’iyyar APC mamaki a jihohin Arewan da ake cewa ta fi karfi.

Gwamna Nasir ya ce ya taba gargadin Waziri Atiku da ya kiyayi Muhammadu Buhari domin a cewarsa babu wani dan siyasa a Arewacin kasar nan da ya kai shi farin jini. A’aha, Gwamna Nasir ya manta ne a shekarar 2007, sa’ilin da yake  bakar adawa da Buhari, ya taba cewa,  Buhari kaya ne a siysance ba kuma yadda za a yi ya ci zabe, kuma ba wanda zai bata kuri’arsa a kansa? To, don Buhari ya daga hannunsa a 2015 ya ci zabe a sabilinsa, shi zai sa a yanzu ya ce ya fi kowa farin jini a Arewa? Ai ga  Arewar  nan,  Shugaba Buhari kuma na nan,  2019 na  nan zuwa. Sai mu jira mu ga  irin rawar da gwamnonin jam’iyyar  APC za su taka wajen bayar da goyon baya ga takarar Shugaba Buhari, hade da yadda  take-taken talakawa a siyasar da za a taka za su canja al’amura, bayan sun kauce wa sak sun rungumi cancanta. Za a kuma zura ido a ga ko  canjin shekar da Waziri  Atiku ya yi zai yi  tasiri ko kuma akasin haka zai kasance? An dai ce dan hakin da ka raina shi zai tsone ma ido.