✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan haya ya harbi makwabciyarsa da bindiga

Ya faki ido ya shiga dakinta ya dirka mata harbi a yayin da take barci.

Wani matashin dan haya ya bude wa makwabciyarsa wuta da bindiga saboda takun saka da ke tsakaninsu.

Wata makwabciyarsu ta ce Adijat Balogun na barci a dakinta ne lokacin da matashin ya faki ido ya shiga dakin ya dirka mata harbi saboda takun sakar da ke tsakaninsu.

Ta ce bayan ya dirka mata harsashi a hakarkarinta na dama sai ya tarkata komatsansa ya arce, kafin jami’ai ’yan sandan da aka kira daga babban caji ofis na Sabo/Ilupeju su iso.

Kakakin ’yan sandan Jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi ya ce, “Bayan ya yi aika-aikan sai ya tarkata komatsansa ya tsere. Sai da aka yi ta farautarsa, da taimakon jama’a aka kama shi a ranar 16 ga Maris, 2021.”

Ya ce da farko matashin ya musanta harbin makwabciyar tasa, amma da aka tambaye shi dalilin tashinsa daga gidan bagatatan sai bakinsa ya mutu.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar ya umarci Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID) na Rundunar su kammala bincike kan lamarin sannan a gurfanar da matashin a gaban kuliya.

Oyeyemi ya ce an kai matar da aka harba Asibitin Jihar da ke Ijaye, daga nan aka tura su zuwa Asibitin Tarayya da ke Abeokuta inda yanzu take murmurewa.