✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan haya ya kashe abokinsa kan N300

Wani dan haya ya caka wa abokinsa kwalba har lahira kan kudin wuta N300.

Wani dan haya ya caka wa abokinsa kwalba har lahira kan kudin wuta N300.

Wanda ake zargin ya caka wa abokin nasa wanda suke hayan daki daya tare wuka ne kan kudin wuta da wani makwabcinsu ya bayar.

A yammacin ranar Juma’a ne kakakin ’yan sandan Jihar Delta, DSP Bright Edafe, ta tabbatar mana da faruwar lamarin, sanna ta ce, “muna kokarin kamo wani wanda ake zargi da hannu a kisan.”

Wannan abun al’ajabi ya faru ne a daren Alhamis a Rukunin Gidaje na Okumagba Layout da ke Karamar Hukumar Warri ta Kudu a jihar.

Wani ganau ya ce rikicin, “Ya samo asali ne a kan kudin wuta N300 da Oke yake tarawa daga ’yan hayar gidan da suke zama, ya kai wa kamfanin wuta.

“A lokacin da ba ya nan ne wani dan haya a gidan ya kawo N300 dinsa ya ba wa abokinsa Allia.

“Amma da Oke ya dawo ya bukaci Allia ya ba shi kudin, sai ya ki, wanda hakan ya sa suka fara dambe.

“Da suke damben ne Oke ya dauko wata fasasshiyar kwalba ya caka wa Allia a wuya, jini ya rika kwarara har ya ce ga garinku nan.

“Yana ganin haka sai ya tsere, ganin yadda mutane suka yi ca a kansa suna neman hallaka shi.”

Ya ce, “Oke ya tsere ne zuwa unguwar Ugborikoko inda aka ’yan sanda suka kama shi.