✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Dan haya ya make maigida har lahira kan kudin haya a Abuja

Wani dan haya ya buge maigidan da yake da zama a gidansa bayan da rikici ya kicime a tsakaninsu kan kudin haya.

Wani dan haya ya buge maigidan da yake da zama a gidansa bayan da rikici ya kicime a tsakaninsu kan kudin haya.

Wannan al’amari ya faru ne a yankin Dakwa da ke Dei-Dei, Abuja, a safiyar Litinin da ta gabata.

Makwabcin dan hayan, Innocent Badmus, ya shaida wa wakilinmu cewa rikici ya soma ne a safiyar wannan rana inda wanda ake zargin ya sa katako ya make maigidan nasu Adegoke Tunde a kai bayan maigidan ya bukaci ya biya shi bashin kudin hanyan da yake bin sa.

Badmus ya ce maigidan ya yi zargin dan hayan ya zage shi wanda hakan ya haifar da sa-in-sa a tsakaninsu.

Ya ce: “Suna tsaka da jayayyar ce sai ya dauki katako ya maka wa maigidanmu a kai, inda ya zube kasa nan take.

“Da ya fahimci abin da ya aikata, sai ya tsere, daga nan makwabta suka kwashi maigidan zuwa asibiti, bayan kwana biyu ya ce ga garinku.”

Sai dai ’yan sandan yankin sun ki cewa komai kan batun.