✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan jaridar Masar ya janye yajin cin abinci

Yana yajin ne saboda fafutukar kafa Dimokuradiyya

Dan jaridar nan dan kasar Masar da Birtaniya da ke rajin kare dimokuradiyya, Alaa Abdel Fattah ya shaida wa danginsa a wata wasika cewa ya kawo karshen yajin cin abinci day a shafe wata bakwai yana yi a cikin gidan kurkukun Masar.

“Ku kawo mini fanke da sauran abincin da kuka saba. Na dakatar da yajina. Zan yi bayanin komai a ranar Alhamis,” ya fadi a wata wasika da aka rubuta ranar Litinin da ta gabata.

’Yar uwarsa ta rubuta sako a shafinta na Tiwita cewa: “Ban san me yake faruwa a cikin (kurkukun) ba.”

Hakan ya zo ne kwana daya bayan danginsa sun samu wasika daga Abdel Fattah cewa ya dawo shan ruwa a ranar Asabar.

Mai shekara 40, Alaa ya fara kin shan ruwa ne a ranar 6 ga Nuwamba daidai da ranar fara taron COP 27 kan yaki da gurbata yanayi da aka gudanar a Sharm el-Sheikh bisa fatar sanya matsi a kan Masar ta bari a kalla jakadun Birtaniya su ziyarce shi.

A ranar Alhamis din makon jiya, mahaifiyarsa ta shaida wa jami’an kurkukun Wadi al-Natroun, da ke Arewacin birnin Alkahira cewa ana “yi masa jinya da sanin mahukuntan bangaren shari’a.”

Masu gabatar da kara a Masar ma sun fitar da wani bayani da cewa rahoton likita ya nuna “lafiyarsa tana da kyau,” ba tare da bayar da wata shaida ba, kamar yadda BBC ya ruwaito.

Abdel Fattah, yana zaman jarun ne na shekara biyar kan zarginsa da “yada labaran karya,” kuma yana daga cikin fitattun fursunonin siyasa 60,000.

Sai dai gwamnatin Masar ta ce babu wani fursunan siyasa a hannunta. Majalisar dinkin Duniya da kasashen Ingila da Amurka da sauran kasashe sun bukaci a sako shi daga kurkukun.