✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan kunar bakin wake ya hallaka dalibai 19 a Afghanistan

An kai harin ne ga daliban da ke shirin rubuta jarabawa

Wani dan kunar-bakin-wake ya kai hari wata makaranta da ke Kabul, babban birnin Afghanistan, inda ya kashe akalla dalibai 19.

Kazalika, harin wanda ya auku da safiyar Juma’a, ya jikkata wasu mutum 27.

Mai magana da yawun ‘yan sandan yankin, Khalid Zadran, ya ce harin ya auku ne a Dasht-e-Barchi, yankin da galibin mazauna cikinsa mabiya mazhabar Shi’a ne.

Jami’in ya ce, “Dalibai na shirin rubuta jarrabawa ne sa’ilin da dan kunar-bakin-waken ya kai wa makarantar hari, inda mutum 19 suka mutu, 27 suka jikkata.”

Bidiyo da sauran hotunan harin da kafafen yada labaran yankin suka yada, sun nuna yadda aka yi ta jigilar wadanda harin ya ritsa da su jina-jina.

Zadran ya ce, bayan aukuwar harin ‘yan uwa da iyayen wadanda abin ya shafa sun garzaya asibitin da aka kai yara, haka nan an lika sunayensu a bango.