✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan kwallon Faransa ya rasu bayan shekara 39 a sume

Ya suma tun shekarar 1982, sannan ya rasu Litinin 6 ga Satumba, 2021.

Tsohon dan wasan kwallon kasar Faransa da kungiyar PSG, Jean-Pierre Adams ya rasu bayan shekara 39 a sume.

A ranar Litinin, Jean-Pierre Adams ya rasu a asibitin Nimes da ke kasar Faransa yana da shekara 73, ya bar matarsa, Bernadette da ta haifa masa ’ya’ya maza biyu.

Tun a shekarar 1982 ne Jean-Pierre Adams, wanda dan asalin kasar Senegal ne ya yi doguwar sumar bayan an yi masa allurar kashe radadi fiye da kima asibiti.

An yi masa allurar ce a lokacin da za a yi masa tiyata a ranar 17 ga watan Mayu, 1982 a asibiitn Edouard Herriot da ke birnin Lyon bayan raunin da ya samu a gwiwarsa.

A garin yi masa allurar sanya barci da kashe radadi ne wata jami’ar lafiay ta yi kuskure inda ta yi masa allurar fiye da kima.

Daga nan dan wasan ya samu matsalar rashin shigar iskar oksijin zuwa kwakwalwarsa, daga baya kuma ya yi doguwar sumar da ya shekara 39 kafin rai ya yi halinsa.

Jean-Pierre Adams
Jean-Pierre Adams a kwance a gadon asibit.

Lamarin dai ya katse wa Jean-Pierre Adams rayuwarsa a fagen kwallon kafa.

A tsawon lokacin da dan wasan ya yi a sume, likitoci sun ba da shawarar a rage masa wahalar rayuwa a yi masa allurar mutuwa, amma matarsa ta ce ta gwammace ta rayu da shi a hakan.

Bayan shekara takwas yana sumen, aka yi afuwa ga jami’an lafiyan da suka yi kuskuren da ya jefa shi cikin wannan halin, aka ci su tarar Dala 815.