✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan kwamitin amintatttun PDP ya bar jam’iyyar

Farfesa Alphonsus Nwosu, na hannun daman Atiku ya fice daga PDP

Mamba a Kwamitin Amintatttun Jam’iyyar PDP, Farfesa Alphonsus Nwosu, ya fice daga jam’iyyar.

Farfesa Alphonsus Nwosu tsohon Ministan Lafiya ne kuma na hannun daman dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Ya bayyana rashin bin tsarin karba-karbar takarar shugaban kasa a PDP a matsayin dalilinsa na raba gari da ficewarsa ita.

Tuni dai ya aike wa Shugaba PDP na Ƙasa, Iyorchia Ayu da Shugaban Riko na Kwamitin Amintatttun jam’iyyar, Adolphus Wabara da kuma shugaban mazabarsa takardarsa ta ficewa daga jam’iyyar.

Farfesa Nwosu na daga cikin iyayen PDP da aka kafa a ta da su.

Ya kuma taka muhimmiyar rawa a mukaman jam’iyyar da ya rike a matakin kasa da kuma yankin Kudu.