✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan kwangilar da ya cinye kudin gyaran gidajen alkalan Kotun Koli ya shiga hannu

Ana zargin shi da cinye kudaden ayyukan da Kotun Koli ta ba shi a 2017

Baban Daraktan kamfanin gini na Asbat Construction, Temitope Banjoko, ya shiga hannun Hukumar Yaki da Almundaha (ICPC).

Wani babban jami’in ICPC da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana wa Aminiya cewa, Bonjoko wanda dan Kwangilar Kotin Koli ne ya shiga hannu saboda zargin sa da almundahanr kudi.

Majiyar ta bayyana cewa kamfanin ya karbi kwangilar rushewa da kwashe baraguzan gidajen wasu alkalai hudu da ke unguwar Maitama a Abuja a shekarar 2017, a kan Naira Miliyan 4,305 har da kudin haraji.

To sai dai duk da kudin sun shiga asusun kamfanin na Asbat, dan kwangilar bai aiwatar da aikin ba, wanda hakan ya sanya Kotun Kolin ta kai wa ICPC kara.

A hannu guda kuma yunkurin da muka yi na ji ta bakin Kakakin hukumar, Misis Azuka Ogugua, kan lamarin ya ci tura, kasancewa mun gaza samun ta a wayar tarho.

Karin bayani na tafe….